Maharan da ake zargin Boko Haram ne na can a lokacin rubuta wannan labari sun kai hari garin Giedam, mahaifar Sufeto Janar Alkali.
Wakilin PREMIUM TIMES ya rika jin rugugin manyan bindigogi a cikin garin, lokacin da ya ke waya da wani mazaunin cikin garin.
“Yanzu ba zan iya magana ba, domin na tabbatar ka na jin karar manyan bindigogi na tashi. Mu yi magana idan komai ya lafa..” Haka wannan mazaunin Giedam ya fada a cikin tsananin firgici.
A ranar 9 Ga Fabrairu, 2021 Boko Haram sun kai farmaki a Girdam, kwana daya bayan ziyarar da sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Ibrahim Attahiru ya kai wa sojoji ziyara a garin.
Kakakin yada labarai na :yan sandan Jihar Yobe Dungus Abdulkarim ya nemi wakilin ya ba shi lokacin da zai binciki lamarin kafin ya waiwaye shi.
Discussion about this post