Cikin watan Juni, 2020, Gwamnan Jihar Ekiti kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi da wasu gwamnoni sun gana da Shugaba Muhammadu Buhari, inda su ka kai masa korafin rashin yardar su da fara aiki da Doka Ta Musamman TA 10 (Executive Order No.10).
Dokar dai ta na nufin cewa za a tsame Majalisar Dokoki ta Jihohi da kotunan jihohi daga karkashin shayarwar Gwamnatin Jihohi, amma a rika dibar kudin su an aba su kai-tsaye daga kudaden da tarayya ke bai wa jihohi a duk wata, ba tare da kudaden na shiga aljihun gwamnatin jihohi daga baya sub a su ba.
Bayan gwamnonin sun fito, Gwamna Fayemi ya shaida wa manema labarai cewa Buhari ya amince ya jingine fara aiki da Dokar Cin Gashin Kan Kotuna da Majalisun Dokin Jihohi, wato dokar da ya rigaya ya saw a hannun amincewa da ita, tun cikin watan Nuwamba, 2018.
A cikin watan Yuni na 2020, Fayemi ya Shugaba ya Muhammadu Buhari ya dakatar da fara tilasta wa jihohin tarayyar kasar nan fara aiki da Dokar Musamman Ta 10, wadda ta bai wa Majalisun Jihohi da Bangaren Shari’a na Jihohi ikon cin gashin kan su gada hannun gwamnatin jihar su.
Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya sanar wa manema labarai haka a ranar, bayan wasu gwamnoni sun gana da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Ministan Shari’a da kuma Ministar Harkokin Kudade.
Fayemi ya ce sun je Fadar Gwamnatin Tarayya domin yin bayanin yadda Buhari zai fahimci cewa Dokar Musamman ta Shugaban Kasa mai lamba 10 da ya rattaba wa hannu, akwai wasu wuraren da ta ci karo da dokar kasa.
Ya ce a kan haka Buhari ya dakatar ko kuma zai yi jinkirin tilasta fara aiki da ita tukunna har sai an warware wuraren da kulli ya cukurkude.
Fayemi ya kara da cewa an kafa kwamiti a karkashin Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal da wasu gwamnoni, inda suke ganawa da Shugabannin Majalisar Jihohi domin fahimtar yadda mishkilar ta ke.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu kan Dokar Cin-gashin-kan Majalisar Dokokin Jiha da Bangaren Shari’a na jiha.
A ranar Juma’a ce kwanaki biyu kafin zuwan gwamnonin ga Shugaba Muhammadu Buhari, ya sa hannu a kan Dokar Musamman ta Cin-gashin-kan Majalisar Dokokin Jihohi da bangaren shari’un fadin kasar nan.
A karkashin wannan sabuwar doka, Buhari ya bai wa Ofishin Akanta Janar na Tarayya umarnin cire wa Majalisar Dokoki ko Bangaren Shari’a kudaden su daga asusun duk wata jihar da ta ki bin wannan umarni.
Wannan doka dai ta na nufin kudaden da gwamnatin tarayya ke bai wa Majalisar Jihohi da bangaren shari’a na jihohi 36 da Abuja, ba su kara makalewa asusun jiha, ana jekala-jekalar sai yadda gwamna ya ga damar bada kudaden.
Kakakin Yada Labarai na Ministan Shari’a, Abubakar Malami, mai suna Umar Gwamdu ne ya fitar da wannan sanarwa, kuma ya aiko wa PREMIUM TIMES, a madadin ministan.
Wannan doka mai suna Doka Ta Musamman Ta 10, Ta 2020, ta bai wa gwamnoni umarnin shigar sa Majalisar Dokokin da bangaren shari’a cikin kasadin kudi, tun tashin farko.
Tuni har an bada umarnin kafa kakkarfan kwamitin da zai aikin shimfida ka’idoji, sharudda, hakki da kan-iyakokin da kowane bangare ke da ikon cin-gashin-kai, kamar yadda dokar Sashe na 121 (3) na Dokar Najeriya ta 1999 ya tanadar.
Wannan doka ta haramta wa gwamnonin jihohi rike wa Majalisar Dokokin Jiha da bangaren shari’ar jihar dukkan hakkokin su.
Kuma dokar ta umarci duk gwamnan da ya ki bin dokar, to a Akanta Janar na Tarayya ya cire kudaden majalisa da na kotuna da alkalan daga kason kudaden da gwamnatin tarayya ke tura wa jihar a duk wata.
Rahin fara amfani da wannan doka ce ta sa Kungiyar Ma’aikatan Kotuna da Fannin Shari’a su ka garzaya yajin aikin da ya tsaida harkokin shari’a kasar nan baki daya.
YAJIN AIKIN MA’AIKATAN KOTUNA: Dokar Cin-gashin-kan Kotuna Tuggun Zaben 2023 Ne Gwamnatin APC Ta Kafa – Gwamna Wike
Gwamnan Jihar Ribas Neysom Wike ya bayyana cewa Dokar Musamman (Executive Order 10) mai lamba 10 da Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa wadda ta bai wa Gwamnatin Tarayya ikon kamfatar kudade daga asusun jihohi ta na bai wa bangarorin shari’u da kotunan jihohi, dokar karfa-karfa ce, wadda ba za ta zame wa dimokradiyya alheri ba.
Wike yay i wannan kalami watannin baya, yayin da ya ke jawabi a Taron Shekara-shekara na Nazarin Dokokin Manyan Laifuka, Wike ya ce ba wani abin alheri ne gwamnatin APC ta kulla ba, sai shirye-shiryen tuggun zabe a 2023 kawai.
Ya ce an ga zabe ya zo shi ya sa gwamnatin Buhari ta wanzar da dokar domin bai wa kotunan jihohi ‘yancin su daga gwamnatin jihohi, amma kuma a lokaci guda za su koma “amshin Shatan gwamnatin tarayya.
”Don ka kafa kotuna amma ba ka sakar masu mara yadda za su yi adalci ba, kamar yadda dokar kasa ta tanadar, ai babu maganar adalci da ‘yanci kenan.” Inji Wike, a wurin taron wanda Gidauniyar Jaddada Sahihiyar Turbar Doka da Oda (Rule of Law Development Foundarion) ta shirya a Abuja.
Da ya ke magana a kan tsaro, ya ce ba a bukatar sai an yi wa dokar kasa kwaskwarima sannan jihohi za su iya kafa jami’an sa-kai da za su rika taimaka wa sauran jami’an tsaro wajen samar da tsaro a jiha.
“Ƴan sandan Najeriya su 372,000 kacal ba za su iya sa-ido a kan ‘yan Najeriya su milyan 195 ba.”
Matsayin Gwamnonin Najeriya Bayan Tafiya Yajin Aikin Ma’aikatan Kotuna:
Gwamnonin Najeriya sun tabbatar da nuna bukatar ganin an bai wa kotunan jihohi ikon ‘yancin karbar kudaden su kai tsaye, amma kuma ba su amince a tsame su daga karkashin jihohi ba.
Gwamna Simon Lalong ne na Jihar Filato ya bayyana haka ga ‘yan jarida, a matsayin sa na wakilin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi, bayan sun gana da Ministan Cikikayya na kasar Faransa, Frank Riester wanda ya kawo ziyara Abuja, Najeriya.
Lalong ya bayyana cewa gwamnoni bas u bukatar sai an kafa Dokar Musamman Mai Lamba 10 Kafin a bai wa kotunan jihohi damar karbar kudaden su kai tsaye.
Discussion about this post