Rundunar Sojin Saman Najeriya ta karyata wani bidiyo da Boko Haram suka fitar yana nuna wai sune suka barbo jirgin saman sojojin Najeriya a dajin Sambisa.
Idan ba a manta ba jirgin yaki na rundunara sojin saman Najeriya ya bace bat a sararin samaniyar jihar Barno a ciki. Wannan mako, a inda aka rasa inda ya shiga. Daga baya ru dynat ta sanar cewa tana ci gaba da nemo inda wannan jirgi ya fada.
Amma kuma bayan haka sai Boko Haram suka fitar da wani bidiyo da ke nuna wai sune suka harbo jirgin.
Boko Haram sun yi ikirarin daukar alhakin harbo jirgin yakin Najeriya, wanda aka bayyana bacewar sa kwana biyu da su ka gabata, a kan hanyar sa ta kai wa Boko Haram farmaki.
Kungiyar ta’addancin Boko Haram ta fitar da wani bidiyo, inda aka nuna mayakan ta na harbin wani jirgin yaki, wanda aka tabbatar cewa shi ne samfurin alpha jet, wanda Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana bacewar sa.
Cikin wannan bidiyo mai tsawon mintina bakwai da sakan 30, an nuno jirgin yakin ya na rikitowa kasa, yayin da Boko Haram su ke harbin sa.
An ga wani mayakin Boko Haram a kan jirgin yakin ya hau ya na magana da Hausa kuma da Turanci.
PREMIUM TIMES ta buga labari a safiyar Juma’a cewa Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta bayyana sunayen sojojin sama biyu da su ka bace tare da jirgin yaki yayin kai wa Boko Haram farmaki.
Kakakin Rundunar Sojojin Sama na Najeriya, Gabkwet ya bayyana sunayen sojojin sama biyu da su ka bace tare da jirgin yakin sojoji a yankin Arewa maso Gabas.
Ya bayyana cewa sojojin saman su biyu akwai Flight Lietanant John Abolarinwa da kuma Flight Lietenant Ebiakpo Chapele.”
Ya ce akwai yiwuwar jirgin na su hatsari ya yi ya fado kasa, amma har yanzu dai babu labarin inda su ke.
A takardar Gabkwet ya ce sai da suka yi wa bidiyon bincike filla-filla, daki daki don gano gaskiyar wannan farfaganda kuma sun gano duk shirya wannan bidiyo aka yi amma ba gaskiya bane wai su ne suka harbo jirgin.
A larshe ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da aiki tukuru domin gamawa da Boko Haram din.
Discussion about this post