Bidiyon da ya nuna sojoji na dukan wasu ‘yan bindiga ya faru a Zamfara ne ba tsakanin hanyar Ife zuwa Ibadan ba – Binciken DUBAWA

0

Zargi – Akwai bidiyon da ke yawo a kafofin sada zumunta mai zargin cewa sojoji sun cafke filani makiyaya masu yin garkuwa da mutane a hanyar da ke tsakanin Ife da Ibadan sun yi musu duka.

Rashin tsaro a Najeriya ya zama babban abun mahawara tsakanin al’umma da ma kafofin yada labarai. Tun shekarar 2009, za’a iya cewa ba mafi yawan kasafin kudin kasar matsalar tsaro ta cinye ba hatta shafukan jaridun kasar labaran da suka fi yawa ke nan. Wannan ne ma ya sa batun tsaro ya kasance kan gaba a cikin batutuwan da ke daukar hankali musamman a lokutan da aka wallafa labaran da suka danganci tsaro. Misali akwai wani hoton bidiyon da ake yadawa a shafukan sada zumunta mai zargin sojoji sun kama wasu filani masu garkuwa da mutane tsakanin titin Ife da Ibadan. Bidiyon ya kuma nuno wasu maza sanye da kayan sojoji suna dukan wadansu marasa riga wadanda bidiyon ke zargi masu yin garkuwa da mutane.

Akwai wani bayanin da aka rubuta a gefen hoton bidiyon mai cewa “sojoji sun cafke wasu Fulani makiyaya a hanyar da ke tsakanin Ife da Ibadan. Sojojin sun batar da kama ne suka yi shigar fasinjoji a motar haya kafin suka kamo su. Sun baro shanunsu a daji.

Wannan bidiyon yana kan manhajar youtube, tun ranar 21 ga watan Janairu 2021. Mutane fiye da dubu daya sun kalla. Wasu da dama kuma sun yi tsokaci a karkashin bidiyon amma babu wanda ya yi tababar sahihancin labarin.

Mutane sun yada bidiyon sau da yawa a manhajan sakonni na whatsapp zuwa kungiyoyi daban-daban. Bidiyon bai bayyana dai-dai lokacin da abun ya faru ba, sai dai ya bullo ne kamar kwanan nan aka yi.

Sarkakiyar da ke tattare da batun tsaro da bayanai na daga cikin abubuwan da ke janyo tashin hankali a al’umma. Musamman idan abu ne da kowa zai iya gani, kamar irin wannan bidiyon da muke magana a kai. Bugu da kari wannan zargi zai iya haddasa rigima sosai bisa la’akari da mahawarorin da ake tabkawa yanzu dangane da kasancewar filani makiyaya a yankin kudancin Najeriya da ma rahotannin kwana-kwanan nan da ke cewa makiyayan sun kai hari a jihar Osun.

A taikaice wannan zai iya ta’azara matsalar rashin tsaro a yankunan da abin ya shafa. Dan wannan ne ma DUBAWA ta ga ya dace ta gano gaskiyar wannan batu musamman ma wurin da ya afku da lokacin da ya afku.

Tantancewa

Da farko, DUBAWA ta duba wani hoton bidiyon wanda hotunan daya ne da wannan sai dai labaran sun dan banbanta da kadan. Shi ma an wallafa shi a manhajan youtube ranar 26 ga watan Yuni a shekarar 2019. Ga bayanin da aka yi a kan wannan bidiyon : Na wani tsawon lokaci yanzu, kadan za’a iya fada gsme da bannar da ‘yan bindiga ke yi a kasar nan. Duk da cwa dakarun sojin Najeriya sun ja musu kunne kan kiwo a gonakin jama’a. Mene ne ra’ayinku dangane da wannan batu? A ko A’A

A yayinda bayanin ke cewa sojoji sun kama makiyayan ne saboda satar mutanen da suke yi su nemi kudin fansa, har ma ya nuna cewa kwanan nan abun ya faru, dayan ya nuna cewa an kama su ne suna kiwo a gonakin jama’a a shekarar 2019. Wadannan bayanai mabanbanta sun sanya alamar tambaya kan lokacin da abun ya faru takamaimai.

Duk da haka DUBAWA ta gano cewa an nadi bidiyon ne a shekarar 2019. Sai dai abin da ya banbanta su shi ne abun ya faru ne a karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara ba a hanyar Ife zuwa Ibadan ba yadda bidiyon ya nuna.

Wani abun mamaki ma shi ne kakakin rundunar sojojin sama Air Commodore Ibikunle Daramola, ya yi Allah wadai da batun a shekarar ta 2019 a wata sanarwar da ya baiwa manema labarai a wancan lokacin inda ya bayyana cewa:

“An ja hankalin sojojin saman Najeriya (NAF) zuwa kan wani bidiyo da hotunan da ake yadawa a shafukan sada zumunta, inda wadansu sojoji ke dukan wasu wadanda ake zargi ‘yan bindiga ne a karamar hukumar Shinkafi, jihar Zamfara. NAF ta gano cewa akwai wadansu daga cikin jami’anta da aka tura wajen kungiyar hadin gwiwar da aka kai Galadi. NAF ta na so ta bayyana cewa abin da dakarun suka yi ba daidai ba ne. Duka ko cin zarafin mutumin da ba ya tare da makami abu ne da ba za mu lamunta ba kuma ko daya bai zo daidai da ka’idojin da muke amfani da su wajen aiwatar da wannan shirin ba.”

Kafofin yada labarai sun yi rahotanni sosai dangane da sanarwar.

Wadansu daga cikin abubuwan da aka nuna a bidiyon ma sun sake ba da tabbacin cewa abun ya faru a yakin arewa maso yammacin kasar ne domin a daidai minti 1:59 daya daga cikin sojojin cewa ya yi. “Mu ba sharan daji ne kadai ba, mu ne operation 777. Operation sharan daji ko 777 sashi ne na dakarun sojojin Najeriyar da aka girka a shekarar 2015 domin ta rika mayar da martani ga kukan da ake yi da ‘yan bindiga, da masu satar shanu da yin garkuwa da mutane a yankin arewa maso yammacin Najeriya tare da mayar da hankali a Zamfara.

Da ma a shekarar 2019, lokacin da abun ya faru, Tolu Ogunlesi mai bai wa shugaba Buhari shawara a kan kafofin sadarwa na yanar gizo ya ba da tabbacin cewa operation sharan daji a wannan yankin take. Wannan na nufin abun bai faru a hanyar Ife da Ibadan ba saboda wannan sashen na sojojin da aka ambata ba a wannan yankin yake ba.

A Karshe

Duk da cewa gaskiya ne wannan lamarin ya afku, bayanin da aka sanya a bidiyon dangane da sadda ya afku ba daidai ba ne. Saboda haka wannan bidiyon tana yaudarar jama’a ne domin abun ya faru a shinkafi, jihar Zamfara ne ba t

Share.

game da Author