BAYAN RUFE GAWARWAKI 90 A MAGAMI: Har yau an rasa inda sauran mutane su ke a Zamfara

0

Yayin da adadin wadanda aka sallaci gawarwakin su su ka kai 90, har yau rahotanni a Jihar Zamfara na nuni da cewa ana cigiyar wasu mutane da dama da ba a gani ba, bayan kisan-gillar da mahara su ka tabka a yankunan Magami da ke cikin Karamar Hukumar Gusau.

Gwamnatin Jihar Zamfara dai ta rufe wasu manyan kasuwannin jihar guda hudu, saboda tsoron kada ‘yan bijilante su kai harin ramuwar-gayya

Rahotannin hare-haren dai na zuwa daga bakin mutanen da aka raba da garuruwan su da kuma wadanda aka tarwatsa wa matsigunai.

Ita dai gwamnatin jihar Zamfara ta yi shiru ba ta bayyana adadin wadanda aka kashe ba, sai dai kawai ta yi kira ga jami’an tsaro su kara kula yankunan da ke fama da barazanar sake iya kai masu farmaki.

Mazauna garin Magami dai a ranar Juma’a da safe sun bayyana cewa sun rufe gawarwakin sama da mutum 60, bayan a ranar alhamis sun bayyana kisan mutum 53 da su ka ce an yi. Sun kuma ce ana ci gaba da neman wasu mutan da dama. Mutanen ana zargin ko dai anyi garkuwa da su, an shiga daji da su, ko kuma an kashe su amma ba a kai ga tsinto gawarwakin su ba.

Babban Limamin Magami, mai suna Sanusi Na’ibi, wanda ya yi wa gawarqakin sallah. An kuma bayyana cewa yawancin gawarwakin an kai su Magami daga cikin wasu kauyukan da ke makwautaka da garin.

Sai dai kuma a cikin wasu lungunan da kai gawarwaki zuwa Magami na da wahala, sun yi wa gawarwakin da aka kashe masu sallah a cikin lungunan kauyukan su, kana kuma su ka rufe su a can cikin kauyukan, ba su kai su Magami ba..

“A Karamar Hukumar Gusau aka fi yin wannan mummunanr aika-aika, inda makasa su ka kashe da dama kuma sace dukiyoyin jama’a.” Haka wata majiya ta shaida wa Premium Times Hausa.

Rufe Kasuwanni:

Kasuwannin da Gwamnatin Jihar Zamfara ta rufe sun hada da Kasuwar Magami cikin Karamar Hukumar Gusau, Kasuwar Dansadau da ke cikin Karamar Hukumar Maru, Kasuwar Wanke cikin Karamar Hukumar Gusau da Kasuwar Dauran da ke cikin Karamar Hukumar Zurmi.

“Gwamnati na kira ga jami’an tsaro su ragargaji duk wanda aka samu ya na karya doka cikin kasuwannin da aka hana ci.” Haka Kwamishinan Yada Labarai, Ibrahim Dosara ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Share.

game da Author