Hargitsi ya barke a gidan kurkukun Bauchi, inda daurarru biyar da jami’an Gidan Kurkuku biyu su ka ji raunuka, kamar yadda Kakakin Yada Labarai na Gidan Kurkukun Bauchi, Abubakar Adamu ya tabbatar.
Adamu ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a cewa hargitsin ya barke sanadiyyar wata harkallar safarar wasu abubuwa da wani jami’in aikin idan kurkuku din ke yi wa wasu daurarru.
“Wata tarzoma ce ta barke a gidan kurkukun na Bauchi, sanadiyyar wata harkallar safarar wayoyin hannu, muggan kwayoyi da wasu kayan laifi da wani jami’in gidan kurkuku ke yi wa wasu daurarru a cikin gidan kurkuku din.
“Abin takaici ya faru ga jami’an tsaron kurkuku din, domin yayin da masu leken asiri su ka damke shi, kuma labari ya kai kunnen daurarrun, sai su ka fasa dakin ajiyar kayyayaki, su ka rarumi diga da cebur.
“Daurarrun nan sai su ka barke da ihu su na rera wakoki, su ka fara farfasa wasu kayayyaki a cikin gidan kurkukun. Wannan ce ta sa tilas jami’ai su ka fara harba bindigogi sama, domin su razana daurarrun har su daina tarzomar.”
Adamu ya kara da cewa amma yanzu komai ya lafa su kuma daurarrun kowa ya koma dakin sa.
Kakakin ya yi kira ga jama’a kowa ya ci gaba da gudanar da harkokin sa lami lafiya.
Manema labarai sun tabbatar da cewa an tsaurara tsaro a gidan kurkukun, kuma an takura gilmawar motoci kusa da harabar kurkukun.
Discussion about this post