BARNO: Boko Haram sun banka wa kayan UN wuta bayan sun kashe sojoji da farar hula a Damasak

0

Akalla mutum hudu cikin su har da sojoji ne Boko Haram su ka kashe a wani mummunan hari da su ka kai a Damasak, gari da ke kan iyakar Jihar Barno.

Majiya ta bayyana cewa Boko Haram ‘yan bangaren ISWAP ne su ka kai wannan hari, inda bayan kashe mutum hudun, sun kuma kai farmaki a kan wasu kayan Majalisar Dinkin Duniya, ofishin ‘yan sanda da kuma wani asibiti.

Wasu bayanai da su ka fito daga garin wanda ke kan iyaka, an tabbatar da cewa ISWAP sun kai harin da a ranar Asabar. Amma dai zuwa yanzu babu wani karin haske game da ko an samu karin asarar rayuka zuwa yau Lahadi da safe.

“Lamarin ya yi muni kwarai da gaske a ranar Asabar, a lokacin da Boko Haram su ka dira Damasak da rana tsaka.” Haka wata majiyar jami’an tsaron sa-kai ta bayyana wa PREMIUM TIMES, kuma ta nemi a sakaya sunan ta.

“Mahara din sun yi jerin gwano ne a kan babura dauke da zabga-zabgan bindigogi wasu kuma na kan motocin yaki.

“Sun kai hari a zansanin ofishin Majalisar Dinkin Duniya, su ka banka masa wuta.

“Sannan kuma sun yi wa wasu mutum biyu yankan rago. Daga baya kuma mu ka gano cewa sun kashe wasu zaratan sojoji biyu.”

“Tabbas kuma sun banka wuta kan wani wuri na Majalisar Dinkin Duniya da GISCOR da INTERSOS da NRC duk da haka kuma su ka saci motoci yayin kai wa sauran wuraren hare-hare.

“Boko Haram sun kuma zarce har Babban Asibitin Damasak su ka yi awon gaba da magunguna da kayan da su ka danganci amfanin majiyyata. Amma a wurin wani Kwamandan su ya hana su banka wa asibitin wuta, saboda akwai marasa lafiya kwance a asibitin.”

PREMIUM TIMES ta gano cewa har ofishin ‘yan sanda na Damasak Boko Haram sai da su ka kai wa hari a ranar.

“Harin da aka banka wa kayan Majalisar Dinkin duniya wuta, ya shafi wasu runbunan ajiyar kayan agaji na wasu kungiyoyi, ciki har da ACTED, duk sun ci wuta.

Majiya ta ce maharan sun arce da motar daukar maras lafiya ta asibitin Damasak da kuma wasu motocin daban.

‘Fashewar Bam a Tsakiyar Mutane’

Wasu ‘yan garin Damasak sun yi ikirarin cewa wani jirgin yaki ya kai dauki, amma an samu kuskure ya jefa bam cikin gungun masu taro radin suna a cikin wani gida, har ya kashe mutane da yawa manya da kananan yara.

Amma dai PREMIUM TIMES ta kasa tantance gaskiyar wannan lamari na jefa bam.

Share.

game da Author