Fitaccen malamin addinin musulunci, mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Ahmed Gume ya gargadi gwamnati da kada ta biye wa karabitin mutane da ke ta zazzabura, suna murza kashin baki, aa su na kira da a tsige ministan Sadarwa, Sheikh Isah Pantami daga minista.
Gumi ya ce a iya sanin sa da Pantami da kuma karantarwarsa, babu abin da ya alakanta shi ta’addanci, a asirce ko a bayyane.
Hasali ma ya ce ‘yan ta’ addan ne ma ke kulla masa wannan makircedon ganin an tozarta shi.
Gumi ya kara da cewa Pantami ya kawo daidaituwa a aikin gwamnati musamman wajen jawo hankalin matasa, da nuna musu alfanun karatun boko da na addini a rayuwa.
” Babu wanda zai iya maida kowa Kirista ko kowa Musulmi a Najeriya. Annabi Isah bai maida kowa Christian ba a duniya, haka Annabi Muhammadu. Wannan ba hurumin mutum bane. Allab ya ce ya halicce mu, dabam dabam kuma haka za a rayu. .
” Babu wani abu da Pantami yake yi da ya nuna wai shi dan ta’adda ne ko yana tare da ‘yan ta’adda. Hasali ma yan Ta’adda ne ke kokarin ganin bayan sa. Kada ya ce zai ajiye aiki ko kuma yayi murabus domin yin hakan babban hadari a wannan lokaci ba gashi ba harda kasa baki daya.
” Pantami yana daidaita gwamnati musamman matasa da suka bibiyar da’awarsa. Kada ku rika cewa a cire shi. Idan kuka yi haka, lallai za ku yi dana sani. Ba shi da alaka da ta’addanci ko ‘yan ta’ adda.
Gumi ya kara da yin kira da nasiha ga matasan malamai masu tasowa da su rika natsuwa suna karatu da fahimtar addini mai zurfi gudun kada su afka cikin rudani, ta yadda wata rana ba za a ce sun ce wani abu ba, su rika cewa ai lokacin ba su da ilimi mai zurfi ne akai.
” Abubuwan da ake zargin sa da cewa, shima ya fito da bakin za ya ce wasu akwai yaranta a ciki. Toh irin haka ne ya kamata malami ya kai lokacin da ya san ya samu ilimi daidai gwargwado kafin ya fara yin da’awa don guje wa haka.
A karshe, Gumi ya ce matsayarsa game da ko Pantami ya cigaba da zama bisa kujerar minista ko kuma ya yi murabus, shine ya ci gaba da aikin sa, sannan ya gargadi gwamnati kada ta biye wa makiyan ministan, domin a gaskiya ganganci ne tsige ministan don bai aikata laifi, kuma duk zarge-zargen da ake yi akan sa karerayi ne kawai. Pantami ba dan ta’adda bane.
Discussion about this post