Ba a raba kudaden tallafin korona a jihohi ‘bil-hakki-da-gaskiya ba’ – Kungiyar BudgiT

0

Wata Kungiyar bin Diddigin Yadda Ake Gudanar da Ayyukan Gwamnatoci Bisa Gaskiya da Adalci, mai suna BudgiT, ta bayyana damuwa dangabe yadda aka raba kudaden tallafin korona a Najeriya.

A cikin wani Rahoton Bincike kan Yadda aka Kashe Kudin Tallafin Korona, BudgiT ta ce ba a kashe kudaden ko raba kudaden ‘bil-hakki-da-gaskiya’ ba.

“Babban misali a nan, a ranar 7 Ga Afrilu, 2020, COCAVID wadda gamayyar kungiyar masu bada tallafi ce, ta karbi gudummawar tallafin kudade naira biliyan 21.5 kamar yadda PROSHARE BUdgiT ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.

“A takaicen takaitawa kenan Gwamnatin Tarayya ta raba naira biliyan 288 daga naira biliyan 500 da ta ce ta kebe waje daya domin bayar da daukin tallafin koronar da zai tsamo tattalin arzikin kasar nan.

“To ya zuwa lokacin da mu ka hada wannan rahoto, Kididdigar Bin Diddigin Bincike ta nuna akwai matukar damuwa dangane da irin yadda aka raba kudaden ba a kan gaskiya ba.”

BudgiT ta ce ta bi diddigin yadda aka kashe kudade a hukumomin da ke da ruwa da tsaki da kudaden da cibiyoyi da kungiyoyi su ka bayar da kuma wasu dala bilyan 5.6 wadanda tallafi ne da gudummawa da ita gwamnatin Najeriya ta ce ta ware ta raba.

Bayan gudanar da wannan bincike, Babban Jami’in Gudanarwa na BudgiT, Iyanuolluwa Bolarinwa ya bayyana cewa kwata-kwata akwa rashin adalci da kuma kin aiwatar da rabon tallafin korona da gaskiya.

Ya yi karin hasken cewa BudgiT za ta taimaka wa Gwamnatin Tarayya wajen bayyana mata komai dalla-dalla, domin a warware, kuma kowa ya ga yadda lamarin ba a shirya shi cikin gaskiya da gaskiya ba.

‘Baba-rodo A Rabon Kudin Korona A Kano, Neja, Lagos, Ogun, Enugu da Ribas’:

BudgiT ta buga misali da kwakkwaran binciken da ta ce ta gudanar a Jihohin Neja, Kano, Lagos, Ogun, Enugu da Ribas, inda ta ce jama’a ba su amince da irin yadda aka yi rabon kudaden tallafin korona a jihohin.

BudgiT ta bayyana cewa a wadannan jihohi ta bi diddigi, amma ta kasa samun marasa galihun da ake cewa su ne aka ce an raba wa kudaden, ballantana ta tabbatar.

BudgiT dai ta ce ta aika wa Gwamnatin Tarayya wasikar nuna damuwa dangane da sakamakon da binciken da ta yi kan rabon tallafin korona a Najeriya.

Saboda haka, kungiyar ta ce ta na jiran amsa daga gwamnatin tarayya kafin ta dauki matakina gaba.

Baya-bayan nan PREMIUM TIMES Ta buga wata dambarwar da faru a kotu, yayin da Minista Sadiyya ta ce tabbas an kashe naira milyan 500 a ciyar da dalibai daga gida a jihohi biyu da Abuja.

A wancan rahoton dai Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, Sadiya Farouq, ta kara jaddada cewa tabbas ma’aikatar ta ta kashe fiye da naira milyan 500 wajen ciyar da ‘yan makaranta a lokacin kullen korona, a jihohi biyu da babban birnin tarayya, Abuja.

Akwai karin bayanai na adadin kudaden da aka kashe, wadanda ministar ta yi dangane da shirin wanda aka aiwatar cikin shekarar da ta gabata.

Yayin da ta ke warware wa jama’a shakkun da su ke yi kan gaskiyar adadin kudaden da ake cewa an kashe, a cikin watan Agusta, Sadiya ta bayyana cewa an kashe naira milyan 523,2733,800 wajen ciyar da ’yan makaranta a jihhin Ogun, Lagos da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.

Yadda Labari Ya Sha Bamban:

Amma a cikin wasu takardun bayanai da aka shigar a kotu, a madadin ta, a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar 26 Ga Janairu, 2021, ta bayyana cewa ma’aikatar ta ta kashe naira milyan 535,873,800, a gidaje 127,789, sabanin naira milyan 523,273,800 a gidaje 124,589 kamar yadda mai shigar da kara wato kungiyar KHFRI ta gabatar wa kotu, inda ta nemi a bayyana masa filla-fillar kudaden da aka kashe a shirin ciyar da dalibai daga gida a lokacin kullen korona.

Yayin da takardun da Ahmed Abdullahi wanda shi ne lauyan ma’aikatar ya gabatar a kotu ke nuni da cewa an dauki masu dafa abinci har su 5,000 a jihohin Oyo da Lagos da Abuja, wadanda kuma su ka yi aikin dafuwar abinci na kwanaki 20 kamar yadda jami’ar gudanar da shirin, Titilayo ta yi masa bayani.

Wannan bayani na sa ya yi hannun riga da bayanin da Minista Sadiya ta yi a cikin watan Agusta, inda ta bayyana cewa ba dafaffen abinci aka raba wa yara ’yan makarantar ba.

Sai dai kuma abin lura a nan shi ne a wadancan kwanaki 20 da aka ce an dauka ana rabon abincin, dukkan makarantu su na kulle, duk da haka an bayyana cewa dalibai 2,859 ne su ka amfana da tsarin rabon kayan abincin a lokacin kullen korona.

Idan za a iya tunawa, wata Kungiyar Kare Hakkin Jama’a mai suna KHRFI ce ta kai Minista Sadiya da ma’aikatar ta kara a kotu, cikin watan Nuwamba, 2011, ta na neman kotun ta tilasta wadanda kungiyar ke kara su bayyana filla-filla wadanda su ka ci kudin tallafin korona a lokacin zaman gida saboda kullen korona.

Kungiyar ta ce ta yanke shawarar maka su kara kotu, saboda ana zargin an yi sama da fadi da wasu daga cikin makudan kudaden.

Sauran wadanda kungiar ta KHRFI ta maka kotu a kan lamarin sun hada Shigaban lKwamitin Shugaban Kasa kan Dakile Cutar Korona, kuma Sak ataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, sai kuma Hukumar ICPC.

‘Yadda Muka Kashe Wa ’Yan Makarnata Naira 535,873,800 A Lokacin Kullen Korona’-Ahmed Adullahi.

Ahmed Abdullahi ya bayyana cewa, “ba kudade ba ne aka rika kwasa ana rabawa ba”, kayan abinci aka rika saye na naira 4,200 ga kowane gida daya, a kan du dan makaranta daya naira 70. Kan kiyasin cewa a kowane gida akwai dan makaranta akalla uku.

Ya ce an yi a makarantu 2,859, dalibai 382,765.

FCT Abuja a gidaje 29,609 sai kuma gidaje 37,589 a Lagos da kuma wasu gidaje 60,391 a Jihar Ogun.

“An yi wannan aikin rabon tallafi a Lagos cikin watan Mayu, daga ranar 21 zuwa watan Yuni 3, 2020.

“A jihar Ogun kuma daga ranar 17 Ga Yuni zuwa ranar 6 Ga Agusta, 2020.

“Na FCT Abuja kuwa daga Mayy 21 zuwa Mayu 29, 2020.

“Shirin ba kudade ya dauka ya raba ba, kayan abinci ya rika rabawa na adadin naira 4,200 a kowane gida da aka kiyasta akwai dan makaranta uku. Sai aka lissafa kowane dan makaranta abincin naira 70, tsawon kwanaki 20 da ake zuwa makaranta a cikin wata daya.

A FCT an yi a cikin kananan hukumomi shida, makarantu 404, inda aka dauki masu dafa abinci 895, aka raba wa ’yan makaranta su 88,826 a gidajje 29,609 a kan kowane gida naira 4,200, inda kudaden su ka kama naira 124,357,800”

“A Lagos an raba a kananan hukumomi 20, masu dafa abinci 1,419, dan makaranta 112,767, sai kuma gidaje 37,689. Kudin su ka kama N4,200 kowane gida, adadin jimilla N157,873,800.”

Sannan kuma ya bayyana cewa ma’aikatar sa ba ta rike bayanai ta ki bayarwa ba, sai dai kawai wanda aka tambaya bayanan ne ba a hannun sa ba a lokacin.

Batun dalilin da ya sa aka ki bayyana adireshi da lambobin wayar wadanda aka raba wa kayan abincin kuwa, ya bayyana cewa, “wannan wasu bayanai ne na wasu daidaikun mutane da aka rika bi a na ba su tallafi daban-daban a madadin gwamnatin tarayyar Najeriya.”

Ya kara da cewa babu wanda ya bada adireshin sa da nufin a fallasa shi a ce ya na karbar agaji ko tallafi.

“Don haka ma’aikatar ba ta boye wasu bayanai ko kadai saboda wasu dalilai ba.”

Amma shi Babban Daraktan KHFRI, Okere Nnamdi, ya fitar da sanarwar manema labarai cewa kokarin kare kai da ma’aiakatar ta yi ba shi da wata hujja abin dogaro sahihiya.

Ya ce ya kamata a ce idan ma ma’aikatar ta kasa bayar da sunayen wadanda aka bai wa tallafin ko lambobin wayar su, to akalla a samu sunayen makarantun da aka ce an raba wa abincin.

Share.

game da Author