Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa na Jihar Kano, Muhuyi Magaji, ya yi rantsuwar cewa, “Wa billahil lazi duk wanda mu ka kama ya boye kaya a lokacin azumi, za mu fasa kantin sa mu kwashe kayan mu raba wa talakawa.”
Magaji ya yi wannan kakkausan gargadin ne a wata hira da aka yi da shi a Gidan Radiyon Freedom a ranar Litinin a Kano, cikin wani shiri mai suna ‘Barka da Hantsi.’
Ya nuna damuwar cewa a lokacin korona masana’antu da dama ba su samu damar iya sarrafa kayayyaki musamman kayan masarufi ba. Saboda haka akwai kayayyakin da har yanzu ba su wadata ba.
Sannan kuma ya kara da cewa sun tattauna da masu masana’antu, musamman na sukari cewa kada su sake su boye sukari ya yi karanci ko su kara farashi a lokacin azumi.
“Haka su ma sauran ‘yan kasuwa ba a mu bari su rika kara farashi a cikin azumi ba. Duk wanda mu ka kama, za mu kwace kayan sa mu raba wa jama’a.”
Haka kuma cikin wata hira da aka yi da shi a wani gidan radiyon, Muhuyi Magaji ya bayyana cewa hukumar sa aikin jama’a ta ke yi na karbar korafe-korafe. Saboda haka duk wanda bai gamsu da ayyukan da ta ke yi ba, dka ta ba shi damar ya garzaya kotu ya maka hukumar ta sa kara.