AZUMIN BANA: An hana yin I’tikafi a masallatai a Najeriya

0

Majalisar Ƙoli ta Musulmi a Najeriya, NSCIA ta sanar da dakatar Itikafi a masallatai a Azumin bana.

NSCIA wanda ke karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Sultan Abubakar Sa’ad ta bukaci masallatai su dakatar da yin I’tikaf lokacin azumin watan Ramadan saboda annobar Korona.

Sanarwar da Majalisar NSCIA ta wallafa a shafinta ta tiwita ta gargadi musulmi da su kiyaye dokokin Korona a lokaci wannan Ibada na Azumin watan Ramadana.

Bayan haka majalisar ta yi kuma yi kira ga al’ummar musulmi su kiyaye matakan rage yaɗuwar korona musamman bayar da tazara tsakani a lokacin azumin Ramadan.

Tuni kwamitin ganin wata a Najeriya ya fitar da sanarwar cewa a ranar Litinin ne za a fara duban watan azumi a ƙasar.

A ranar Talata kuma Al’ummar Musulmi ke fatan soma Azumin watan Ramadan.

Mahukunta a kasar Saudiyya sun sanar da rage yawan raka’o’in sallar Taraweeh daga 20 zuwa 10 a Azumin Ramadan din bana.

Bayan haka kuma za mahukuntan sun sanar cewa ba za ayi Itikafi a masallatan biyu ba.

Sarki Salman na Saudiyya ya bayar da umurnin haka kamar yadda jaridar Saudi Gazette tavruwaito.

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais, wanda shine shugaban da ke kula da masallatan biyu, ya ce za a rage yawan raka’o’in zuwa 10 daga 20 da aka saba yi.

Sannan za a yi Sallar ne bisa bin ka’idojin da aka gindaya na kariya daga kamuwa da yada cutar Korona.

Al’umman musulmi a duniya za su tashi da Azumi ranar Talata in Allah ya kaimu.

Za a kwashe kwanaki 29 ko 30 ana ta Ibada ga Allah.

Share.

game da Author