Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar ya yi kira ga musulmai najeriya da su dage da yin addu’o’i a lokacin azumin watan ramadan.
Sultan Abubakar ya bayyana haka a lokacin da yake sanar da ganin watan ramadana na wannan shekara.
” Ina horon musulman kasar nan su dage da addu’o’i a wannan wata na ramadan wanda za fara ranar Talata.
Sannan kuma a bana an umarci musulmi kada su yi zaman I’tikafi wanda akae yi a masallatai saboda kiyaye dokokin annobar Korona.
Bayan haka shima shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga yan Najeriya su yi amfani da wannan lokacin na azumin Ramadan wajen yin addu’o’i, Allah kara hada kan yan kasa, ya kau da matsalolin da kasar ke ciki.