Sanata Uba Sani dake wakiltar Kaduna ta Tsakiya ya hori musulmai su dage da yin addu’o’i wa kasa Najeriya da kuma yi wa al’umman musulmai fatan Allah yasa a yi Azumin watan Ramadana lafiya.
Sanata Sani ya bayyana cewa wannan watan rahama wata ce da dukka musulmai suke dukufa wajen tsananta bauta zuwa ga Allah da kuma yin addu’o’i.
” Muna fatan za a fara Azumi lafiya a kuma ga lafiya. Allah ya kara mana zaman lafiya a kasa baki daya da jihar mu, jihar Kaduna.
” Ina yin kira da godewa mutanen mazabar Kaduna Ta Tsakiya bisa goyon bayan da suke bani a matsayin sanatan su da kuma mutanen jihar Kaduna gaba daya.
“Allah ya sada mu da dukkan Alkhairan dake cikin wannan wata na Ramadana”
Discussion about this post