APCn Bauchi sun gwasale gwamna Bala, sun maida masa tallafin Azumi da ya aiko wa jam’iyyar

0

Sakataren hulda da jama’a na jam’iyyar APC a jihar Bauchi Adamu Aliyu-Jallah ya bayyana cewa APC ba ta fatarar da sai ta jira wani a jam’iyyar PDP ya aiko mata tallafi a watan Ramadan.

Jam’iyyar PDP ta aika wa jam’iyyar adawa a jihar wato APC tallafin kayan abinci don rabawa ‘yan jam’iyar a cikin wannan wata na Ramadan da ake ciki.

Sai dai isar wadannan kayan tallafi ke da wuya ofishin APC na jihar sai Aliyu-Jallah, ya ce jam’iyyar ba za ta karbi wannan tallafi ba su tattara abinsu su koma da su.” Mu ba irin halin mu ba ne karbar iriun wannan kyauta ko maula.

” A shekarar bara me ya sa basu aiko mana da wannan tallafi ba sai yance sauran rubabbun kayan tallafin Korona da suka rage shine za su kawo mana mu raba wa mutane.

A karshe Aliyu-Jallah, ya ce jam’iyyar APC ba ta karbar sidin PDP, saboda haka, su tattara can su kara gaba da tarkacen su, ba ma so.

Share.

game da Author