APCn Akwa Ibom ta ki amincewa Minsta Akpabio ya zama jigon jam’iyyar a jihar su

0

Jam’iyyar APC reshen Jihar Akwa Ibom ta ki amincewa da wakkala wa Minsta Godswill Akpabio zama jigon jam’iyyar a jihar.

Wannan lamari ya janyo barkewar jam’iyyar zuwa gida biyu, tsakanin masu goyon bayan sa, da wadanda su ka tuma tsalle gefe daya su ka ki amincewa da shi.

An samu wannan matsala a Jihar Akwa Ibom, yayin da jam’iyyar mai mulki ke ta kokarin ganin ta kara shiri da kimtsi domin tunkarar zaben 2023.

Wadansu jiga-jigan jam’iyyar APC ne jihar ne su ka ki amincewa da ministan a matsayin jigon jam’iyyar su a jihar.

APC ta dare gida biyu a Jihar Akwa Ibom, inda bangare daya na goyon bayan Minista Akpabio, daya bangaren kuma ya na goyon bayan John Akpanudoedehe, wanda tsohon sanata ne, kuma shi ne Sakataren Riko na Kasa na Jam’iyyar APC a yanzu.

Shi dai Akpanudoedehe na shirin fitowa takarar gwamnan jigar Akwa Ibom a karkashin jam’iyyar APC, a zaben 2023. Sai dai kuma akwai alamun da ke fitowa a fili cewa Akpabio ba zai goyi bayan sa ba.

Yayin da bangaren magoya bayan Akpabio su ka yi taro cikin makon da ya gabata a Uyo babban birnin jihar AkwaIbom, sun kaddamar da Ministan Harkokin Bunkasa Neja Delta, Godswill Akpabio a matsayin jigon su.

Sai dai kuma wasu jiga-jigan APC na jihar sun kira wani taro daban domin nuna kin amincewa da fawwala jagorancin APC ga Akpabio a matsayin uban jam’iyyar na Jihar Akwa Ibom.

Hakan na nunfin sun jaddada hukuncin da Majalisar Zartaswar APC ta Jihar ta yanke cewa ta soke jagorancin uban jam’iyya da aka nada wa Akpabio rawani a baya.

Wadanda su ka bijere wa Akpabio sun hada da Akpanudoedehe, Umana Umana, Ita Enag da Effiong Akwa.

Share.

game da Author