APC ta siyar da fom din takarar shugaban karamar hukuma da Kansiloli a jihar Kaduna

0

Kakakin jam’iyyar APC, Tanko Wusono ya bayyana wa manema labarai cewa jam’iyyar APC ta siyar da fom din neman takarar kujerun shugaban karamar hukuma da Kansiloli 905.

Wusono ya ce jam’iyyar ta fara saida fom tun 2 ga Afirilu inda a ka siyar da fom din shugaban karamar hukuma kan naira miliyan 1.1, na kansila kuma naira 310,000.

” Yan takara 105 suka siya fom din takarar kujerar shugaban karamar hukuma na kananan hukumomi 23 dake jihar Kaduna.

” Yan takara 800 suka siya fom din kujeran kansila a mazabun kansiloli 255 a jihar. Babu mace ko daya da ta siya fom din takarar shugabar karamar hukuma, sai dai an samu mata 12 da suka siya fom din takarar kansila. Akwai nakasassu biyar da suka karbi fom din suma.

Sannan kuma karamar hukumar Kaduna ne kadai mataimakin shugaban karamar hukumar zai buga da shugaban karamar.

Duka ciyamomin da ke kan kujerun mulki na kananan hukumomin sun fito takara.

Jam’iyyar APC ta samu sama da miliyan 300 wajen siyar da fom din takarar kujerun karamar hukumar jihar.

Za a yi zaben kananan hukumomin jihad Kaduna ranr 5 ga watan Yuni.

Share.

game da Author