APC ta sake kara wa’adin sabunta rajista da tantance ’yan jam’iyya

0

Duk da jam’iyyar APC ta yi ikirarin cewa ta yi wa ‘yan Najeriya sama da miliyan 35 rajista a karkashin jam’iyyar APC, yanzu kuwa a karo na biyu ta kara wa’adin ci gaba da yankar sabuwar rajistar jam’iyyar tare da tantance ‘ya’yan jam’iyyar a fadin kasar nan.

Cikin wata sanarwa da Sakataren APC na Kasa John Akpanudoedehe ya fitar, ya bayyana cewa an kara wa’adin makonni uku, tun daga ranar 1 Ga Afrilu.

Cikin makonni biyu da su ka gabata, Gwamnan Jihar Jihar Jigawa Adubakar Badaru ya bayyana cewa APC ta yi wa mutum milyan 35 rajista a cikin jam’iyyar.

Sai dai kuma jama’a da dama sun rika tababa, shakku da karyata ikirarin na sa, su na kafa hujja da yadda ba a ganin cinkoson jama’a wurin yin rajistar.

A Kano, wakilin mu ya rika cin karo da katin sabunta rajistar APC ana zuwa kosai, soyayyen kifi ko nama balangu da tsire a ciki.

Wannan a cewar wasu da dama, ya nuna kenan dimbin takardun sabunta rajistar APC sun yi kwantai saboda ba a samu masu zuwa sabunta rajistar da yawa kamar yadda jam’iyyar ta yi ikirarin cewa har mutum miliyan 35 ne su ka sabunta rajistar a fadin kasar nan.

Tun da farko dai an shirya za a dakatar da aikin sabunta rajistar a ranar 8 Ga Maris, bayan an fara amma sai aka kara wa’adi zuwa 31 Ga Maris, sakamakon matsalolin da aka fuskanta a jihohi daban-daban.

Da ya ke bada dalillin sake kara wa’adin yin rajistar, kakakin jam’iyyar na kasa ya ce an yanke shawarar karin wa’adin ne saboda la’akarin da aka yi ganin yadda dimbin jama’a ke ta rokon a ba su damar yin rajista cikin jam’iyyar APC mai dimbin farin jini a kasar nan.

Share.

game da Author