An yi nadin sabon sarkin Dangulbi dake Jihar Zamfara

0

Alhaji Hussaini Marafa, shi ne sabon uban kasar Dangulbi dake a masarautar Dansadau a karamar hukumar Maru a Jihar Zamfara.

Maimartaba Sarkin Dansadau, Alhaji Husseini Umar shi yayi nadin a fadarsa dake garin Dansadau a ranar Talata.

Nadin ya samu amincewar gwamna Bello Matawalle na Jihar ta Zamfara.

Alhaji Marafa shi ne sarki na goma, ya gaji mahaifinsa Shehu Umar, wanda ya rasu a ranar 28/12/2020 bayan ya kwashe shekara 31 yana mulkin Dangulbi.

Kakan sabon sarki Marafa, maisuna Umar Garaccin shi ne sarkin Dangulbi na takwas shi yafi dadewa a karagar mulki, yayi shekara 38 yana uban kasar Dangulbi.

Bikin nadin ya samu halalcin Sarkin kudun Dansadau, da maigirma kantoman riko na karamar hukumar mulkin Maru, Salisu Isah, matawallen Dansadau da sauran manyan baki.

Sabon uban kasar zaiyi fama da Matsalar tsaro da ya shafi rikicin manoma da makiyaya da yankin na Dansadau ke fama da shi sawon shekaru.

Share.

game da Author