Mutum biyu sun mutu, rumfuna 200 sun kone kurmus a gobarar da aka yi a sansanin ‘yan gudun hijra dake Gajiram jihar Barno.
Shugaban sansanin Gajiram Malam Bashir ya ce babu wanda ya san sanadiyyar tashin wannan gobara.
Ya ce sau biyu kenan wuta na tashi cikin kwana daya.
Wasu mazauna sansanin sun ce bayan awa 48 da aukuwar gobarar har yanzu shiru suke ji game da aiko musu da kayan tallafi daga bangaren gwamnati.
Da yake mafi yawan ‘yan gudun hijiran dake zama a sansanin Gajiram musulmai ne da dama daga cikin su sun ce basu san yadda za su yi azumin Ramadan ba saboda gobaran ta cinye dan abincin da suke da shi da wurin kwanciyar su.
Har yanzu dai hukumar bada agajin gaggawa ta jihar bata ce komai ba game da aukuwar gobarar.
Discussion about this post