Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa jami’an tsaro sun kara ceto dalibai biyar daga cikin wadanda mahara suka yi garkuwa da su a Kaduna.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya sanar da haka a taron da ya yi da manema labarai ranar Juma’a a garin Kaduna.
Aruwan ya ce tuni gwamnati ta damka daliban ga iyayensu bayan likitoci sun duba su a asibiti.
Idan ba a manta ba a watan Maris ne PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda mahara suka sace dalibai 39 daga makarantar Koyan aikin gona da gandun dazuka, dake Afaka, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna.
Bayan haka a wannan makon gwamnati ta sanar cewa sojoji dake sintiri a dazukan Kaduna sun ceto dalibai biyar daga cikin daliban da mahara suka yi garkuwa da su daga wannan makarantar.
Gwamnati ta ce za ta kara sa himma wajen ganin an kubutar da sauran daliban dake hannun maharan.
Sai dai kuma a daidai ana ta korafin banzatar da daliban da gwamnatin Kaduna suka yi, Gwamnan Jihar Nasir El-Rufai, ya kara jaddada cewa gwamnatin sa ba zata biya kudin fansa ba ko da ko dan sa ne aka sace.
Ya bayyana cewa ba ya tare da wasu gwamnonin da ke ganin biyan kudin fansa shine mafita ga hare-haren yan bindiga a kasar nan.