A ranar Asabar ne aka canja wa gawar Fir’auna da na sauran sarakunan kasar Masar wanda suka mulki duniya tun kafin zuwan Annabi Isah AS.
An nuno wasu motoci na musamman da aka kera su domin daukar wadannan gawarwaki zuwa sabon ginin da aka gina domin ajiye su. Sannan kuma da mata sun yiado kamar wadanda ake nunawa a tarihi ma’aikatan fadar Sarakunan, har da Fir’auna.
An yi wannan buki ne ranar Asabar 3 ga Afrilu.
Mutanen gari da baki daga kasashen duniya sun ziyarci kasar domin ganin wannan abin tarihi da Masar ke tunkaho da shi.
Baya ga saka kowacce gawa a cikin motar zinari an yi musu fareti da karrama su cikin tsattsaurar yanayi na tsaro. Wannan biki ya kasaita matuka.
Kasar masar ta ce ta na karrama wadannan gawarwaki ne a matsayin arziki na gtarihin kasar wanda duk funiya babu kasa mai irin wannan tarihi.
Kasar Masar kasa ce wanda Annabawa da dama suka zauna suka yi mulki a cikinta tun kafin zuwan annabi musa.
Ciki akwai sarakunan kasar Mata guda hudu wanda suka yi mulki a zamanin fir’aunonin da suka gabata a kasar.
Discussion about this post