Duk wani mazaunin Kaduna musamman unguwar Barnawa yana da tarihin wannan masallaci na Juma’a da Idi.
Wannan masallaci na da dimbin tarihi sannan kuma ba tarihin dake tattare da masallacin ba kawai, yana daga cikin manyan masallatan juma’a da suka dade kuma suka yi fice wajen karantar da yara ilimin addinin musulunci a jihar Kaduna, musamman ga wanda ya zarce shekaru 40 zuwa sama, ya san da haka.
Daya daga cikin babban malami a jihar Kaduna kuma fitaccen malami da ya karantar a wannan masallaci da makaranta shine marigayi Imam Lawal Mai-Iyali sannan Kuma akwai Liman Malam Adamu wanda shima ya na daga cikin limamai a wannan masallaci wanda dasu aka kafa wannan masallaci tun a farko. Akwai su malam Munnir, Mal Aliyu, Malam Tukur, Mal Ibrahim Jangebe da dai sauransu wasunsu wanda sun rigamu gidan gaskiya, Allah ya gafarta musu.
Duk wanda ya rayu a wannan unguwa na Barnawa Low cost musamman wanda ya haura shekaru 40 zuwa sama ba zai manta da irin gudunmawar da Malam Dayyibu ya bada a wannan masallaci musamman wajen kula da masallacin a wancen lokaci, kuma yana da ga cikin ladanai na farko a wannan masallaci.
Wadanda ko suka bada gudunmawa domin ci gaban wannan masallaci tun a wancan lokaci, ba su kirguwa, kadan daga cikin wadanda ba za a manta da irin gudunmawar da suka bada a lokacin ba sun hada da Marigayi Mohammed Metcho, Asheikh Jarma, Mal Lawal Ismail, Alhaji Abubakar, da dai sauransu. Wannan masallaci yana da dimbin tarihi a rayuwar mutane da dama.
Baya ga masallaci tun a can baya an somo ta ne da makaranta na Islamiyya, daga baya aka kafa makarantar Boko.
Yanzu duk wadannan makarantu sun zamo zakarun gwajin dafi. Sun yaye dalibai da dama wadanda sun zama shahararrun malaman addinin islama da boko a fadin kasar nan, da kuma manyan ma’aikata.
Ba za manta da irin gudunmawar da matasa suka bada wajen cimma wannan nasara ba, musamman irin su sarkin Samari, AbdulAziz Mukhtar, Hon Habibullah Idris da dai sauransu.
Haka nan shima babban limamin masallacin na yanzu, Imam Bello Mai-Iyali, da sauran al’ummar wannan unguwa da wajen Barnawa duk sai dai ace musu Allah ya saka da Alkhairi.
Allah ya ci gaba da daukaka wannan masallaci da makaranta ya yi mata albarka.