An bude bangaren sufurin jiragen sama na matafiya kasashen waje na filin jirgin saman Aminu Kano

0

Gwamnatin tarayya ta sake bude bangaren sufurin jiragen sama na matafiya kasashen waje na filin jirgin saman Aminu Kano ranar Talata.

Wannan bangare da ake kira ‘International’ ya far aiki nan take ne.

A baya gwamnatin tarraya ta sanar da cewa za’a bude bangaren matafiya kasashen waje na filayen jiragen saman Enugu, Kano da na Fatakwal.

Minista Hadi Sirika yace za’a bude bangaren matafiya kasashen waje na filin jirgin saman Enugu a ranar 3 ga Maris 2021, Kano a ranar 6 ga Afirulu, 2021 sai kuma Fatakwal a ranar 15 ga Afirilu, 2021 domin ci gaba da jigilar matafiya kasashen waje.

Ayau Talata wakilinmu ya shaida saukar jirgin sama na Ethiopian Airline wadda ya sauka da rana, inda ma’aikata da wasu mutanen gari suka bayyana farin cikinsu bayan fiye da shekara daya da rufe wannan bangare.

Share.

game da Author