Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta bayyana cewa, ta kammala Sake Nazarin Farashin Kudin Wutar Lantarki, wadda ta ke raba wa dukkan kamfanonin sayar da wutar lantarki 11 masu zaman kan su, wadanda aka fi sani da ‘DisCos’.
NERC ta fitar da wannan sanarwa a ranar Litinin, cikin wata sanarwar da ta yi ga kamfanonin sayar da wuta, masana’antu da kuma jama’a masu amfani da lantarki baki daya.
Hukumar ta NERC ta ce sake nazarin farashin kudin wutar lantarki ne bisa ka’idar da Dokar Farfado da Makamashi ta EPSRA ta shimfida.
NERC ta kara da cewa an sake nazarin daidaiton kudin wutar ne ta yadda musamman za a kara samun daidaiton adadi, farashi, yawa da karfin wutar lantarkin da masana’antu za su rika samu ta yi daidai da sikelin mizanin ‘iyar-kudin-iyar-shagalin-ka.
Daga nan NERC ta ce cikin watsn Yuli, 2021 za a sake Karamin Fasalin Farashin Wutar Lantarki na shekarar 2020. Dama kuma a duk bayan watanni shida ake nazarin wannan farashi.
Sake nazarin farashin kudin wutar zai yi la’akari ne da tsadar rayuwa, tsadar farashin dala da sauran kudaden kasashen waje masu daraja, farashin gas wanda ake zuba wa injinan bada karfin wutar lantarki da kuma adadin yawan wutar da ita NERC za ta iya samarwa.
Kwanan baya PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin durkushewar tashoshin bada wutar lantarki 18 na kasar nan.
Yayin da wasu su ka lalace, an sanar cewa sauran na fama da karancin gas wanda ake zuba wa injinan badawa da raba wuta a fadin kasar nan.