Akwai akalla manyan makamai miliyan 6 dake yawo a hannun mutane a kasar nan – Abdussalami Abubakar

0

Tsohon shugaban Kasa Abdussalami Abubakar ya bayyana cewa daya daga cikin hadarin da kasar nan ke shine irin yadda manyan makamai suka karade kasar nan.

Abdussalami ya ce akwai akalla manyan makamai da ke hannun mutane a Najeriya da kasashen dake makautaka da ita. Sannan ya kara da cewa dalilin matsalolin rashin tsaro akwai akalla mutum 80,000 da suka rasa rayukan su, kuma mutum sama da milyan uku sun rasa matsuguni.

Abdussalami ya kawo jerin matsalolin da suka addabi Najeriya musamman a bangaren rashin tsaro da suka hada da Boko Haram, masu garkuwa da mutane, ‘Yan bindiga, fashi da makami da sauransu.

” Dalilin wannan taro shine mu tunatar da kan mu game da wadannan matsaloli da kuma lalubo hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen wannan matsaloli da suka addabe kasar. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san da wannan taro da muke yi.

Najeriya ta fada cikin halin matsanancin rashin tsaro a tsawon shekarun nan. Wannan matsala na rashin tsaro ya yi matukar tsanani a Najeriya.

Manyan hanyoyin kasar sun zama abun tsoro, kusan kullum sai anyi garkuwa da mutabe ko kuma ‘yan bindiga sun kashe matafiya.

Ba anan abin ya tsaya ba rashin tsaro ya kaiga har garuruwa mahara ke afka wa su kashe mutane kuma su yi garkuwa da wasu.

Share.

game da Author