Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta bayyana cewa, ba kamar yadda rahotannin da kafafen yada labarai su ka buga cewa sojoji sun yi zanga-zangar fushin biyan su alawus da rashin wadatattun makamai na zamani ba, sojojin sun dan nuna fushin su ne kawai, amma ba wani abin tayar da hankali ba ne.
Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya Mohammed Yerima, ya bayyana a ranar Juma’a cewa kafafen yada labaran da su ka nuna cewa wata bataliya daga Rundunar ‘Operation Lafya Dole’ ta yi zanga-zangar nuna rashin jin dadin biyan su hakkin kudaden alawus da rashin wadatattun makamai na zamani ba, ya ce jaridun ba su bayyana takamaimen gaskiyar abin da ya faru ba.
Yerima ya ce wani dan nuna bacin rai ne kawai sojojin Kar-ta-kwana na MST su ka yi, wadanda ke artabu a karkashin ‘Exercise Tura Takaibango’.
Su dai zaratan ‘Tura-ta-kai-bango, su ne a sahun gaban kai farmaki ga Boko Haram.
Yerima ya bayyana cewa, abin da ya faru, “wajen karfe 3 na yammacin ranar Alhamis, 25 Ga Maris ne wasu sojojin MST 10 DA 11, wadanda ke yaki a karkashin fuskta ta biyu ta TURA TAKAIBANGO a Bama, su ka fito su ka nuna wata damuwar su.
“Kuma nan da nan an kawar masu da damuwar, inda nan da nan kuma su ka nausa su ka ci gaba da aikin su.
“Batun tsoffin makamai kuwa kamar yadda wasu kafafen yada labarai su karuwaito, to matsayar hukumar sojojin Najeriya ita ce sojoji na da ‘yancin da za su nemi a ba su makamai masu inganci da za su yi yaki da su.
“Amma kuma Gwamnatin Tarayya na bakin kokarin ta wajen ganin ta kawo sabbin makamai wadanda za su taimaka wa wadanda ake amfani da su a fagagen dagar yaki da Boko Haram.
“Hukumar Sojojin Najeriya ta na mai karyata duk wani rahoton da ya ce akwai wani soja ko da guda daya tal da ke bakin daga mai bin bashin alawus din sa da ba a biya shi ba”. Inji Yerima.