Shugaban kwamitin dakile yaduwar korona na jihar Tijjani Hussaini ya bayyana cewa gwamnati ta ware wasu asibitoci har 509 da za a rika tsira wa mutanen Kano alluran.
Hussaini ya ce asibitin Dala, asibitin Aminu Kano da asibitin Muhammadu Abdullahi Wase na daga cikin asibitocin da gwamnati zaɓa domin aikin yin rigakafin Korona.
Hussaini ya ce gwamnati ta rarraba yadda za a yi wa mutane allurar rigakafin zuwa gida hudu.
A farko za a yi wa jami’an lafiya da jami’an tsaro, sune za a fara yi wa rigakafin.
Daga nan sai ma’aikatan lafiyan da basu yi allurar rigakafin ba a rukunin farko da tsofaffin da suka dara shekaru 50 duka su ne yan rukuni na biyu.
A rukuni na uku kuma za a yi wa duk mutanen dake fama da wasu cututtuka a jikin su wanda ba Korona.
Sannan sai a yi wa sauran mutane allurar rigakafin a rukuni na hudu.
Ya kuma ce gwamnati za ta yi amfani da matakan da ta tsara a lokacin yi wa yara allurar rigakafin cutar Shan inna idan za a fara yi wa mutane allurar rigakafin Korona a jihar.
Wani likita kuma farfesa dake aiki a asibitin Aminu Kano, Mukhtar Gandanya ya karyata cewa da ake yi rigakafin na yi wa mutane lahani idan aka yi shi.
Ya ce maganin garau yake babu wani illa da ya ke yi wa mutane.
Discussion about this post