Yunwa ta darkako Arewacin Najeriya da wasu kasashe 20

0

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta yi gargadin cewa yunwa ta darkako Arewacin Najeriya da wasu kasashe 20 daban-daban na duniya.

Wasu kasashen da hukumar ta FAO ta yi gargadin cewa yunwa ta nausa kuma ta darkaka sun hada da Afghanistan, Yemen, Congo, Sudan, Habasha, Haiti da Syria.

Wadannan kasashe 20 da hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta lissafa, ta ce nan da ’yan watanni za su iya fadawa cikin halin matsananciyar yunwa, idan ba a gaggauta yin wani kokarin cetar da yankunan ba.

Rahoton wanda na hadin-guiwa ne tsakanin FAO da Cibyar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP), ya kuma yi nuni da cewa

Nan da watan Yuli wadannan kasashe za su shiga matsanancin karancin abinci, don haka akwai bukatar samar da tallafin gaggawa a wuraren da ake ganin matsalar za ta fi shafa matuka.

Rahoton ya danganta kazamin rikicin da ake yi tsakanin Yemen da Saudiyya ne zai jefa wani yanki na kasar Yemen cikin matsanciyar yunwa da karancin abinci.

“Sama da mutum miliyan 16 a kasar Yemen ka iya fuskantar matsanciyar yunwa da karancin abinci musamman zuwa cikin watan Yuni, 2021.

A Arewacin Najeriya kuwa, rahoton ya ce ana tsoron karancin abinci tsakanin watannin Yuni, Yuli da Agusta, sakamakon rikice-rikicen ’yan bindiga da Boko Haram a Arewacin Najeriya.

Rahoton yace matsalar da aka fuskanta a shekarar da ta gabata, za ta iya nunkawa a wannan shekara.

“Nan da watanni shida akalla mutum miliyan 13 za su iya afkawa cikin gagarimar matsalar karancin abinci da matsananciyar yunwa a Arewacin Najeriya.” Haka dai rahoton ya tabbatar.

Dama kuma kusan mutum milyan 32 na rayuwar ‘ya-mu-samu-ya-mu-sa-bakin-mu’, kamar yadda rahoton ya jaddada.

A cikin rahoton, Babban Daraktan Abinci na Hukumar FAO, QU Dongyu ya bayyana cewa matsalar da ta tunkari wadannan kasashe abin tayar da hankali ce matuka.

“Ya zama wajinin mu a tashi a gaggauta yanzu-yanzu domin hakan zai iya cetar rayuka dama, kuma za a hana barkewar mummunar matsala.” Gargadin Dongyu kenan.

Share.

game da Author