‘Yan Najeriya sun fara rige-rigen yin rigakafin Korona, an yi wa mutum sama da da 500,000

0

A ranar Lahadi ne hukumar NPHCDA ta bayyana cewa an yi wa mutum sama da 500,000 allurar rigakafin cutar korona a Najeriya.

Bisa ga bayanan da hukumar ta fitar ya nuna cewa an yi wa mutum 513,626 allurar rigakafin korona a jihohi 35 a kasar nan.

Shugaban hukumar NPHCDA Faisal Shu’aib ya ce har yanzu dai jihar Kogi bata fara yi wa mutanen ta allurar rigakafin korona ba.

Shu’aib ya ce hakan ya biyo bayan rashin samar da wuraren ajiye maganin rigakafin da daukan ma’aikatan da za su yi wa mutane allurar rigakafin.

Ya ce Jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda aka yi wa allurar rigakafin da mutum 110,042.
Daga Nan zai jihohin Ogun-47,507, Kaduna-38,063, Bauchi- 32,482, Katsina- 28,918 da Kwara- 26,473.

Jihohin Abia-22, Taraba-111 da Kebbi-532 sune jihohin da suka fi samun mafi kankantan yawan mutanen da aka yi wa rigakafin korona.

Idan ba a manta ba a ranar Juma’an da ya gabata ne hukumar NPHCDA ta bayyana cewa an yi wa mutum 374,585 allurar rigakafin korona a kasar nan.

Sannan a ranar Laraban makon da ya gabata hukumar ta ce an yi wa mutum 122,410 allurar rigakafin korona.

Shu’aib ya ce har yanzu babu wani rahoton samun matsala ko da daya ne a kasar nan da aka fara yi wa mutane rigakafin korona.

Shu’aib ya yi kira ga yan Najeriya musamman masu fama da wasu cututtuka wanda ba Korona ba su garzayo wuraren da ake yin rigakafin Korona ayi musu.

ya ce hukumar za ta yi kafada-da-kafada da Hukumar NAFDAC domin sa-ido kan allurar da kuwa wadanda ake wa allurar, domin ganin ko da za a samu wani rahoton wanda ya fuskanci wata matsala.

An kawo akalla kwalaben rigakafin AstraZeneca guda milyan 4 a Najeriya.

Haka kuma shima kamfanin MTN ta kawo wa Najeriya kwalaban maganin rigakafin cutar 300,000 ranar Lahadi.

Sai dai kuma yayin da ake ci gaba da yin allurar ta AstraZeneca a Najeriya, wasu kasashe da su ka hada da Jamus, Italy, Faransa, Netherlands, Ireland, Austria, Afrika ta Kudu da sauran kasashe da dama irin sun dakatar da yi wa al’ummar kasashen su rigakafin AstraZeneca, biyo bayan rahotannin cewa allurar na haddasa toshewar magudanan jini a cikin jikin wanda aka yi wa allurar.

Zuwa yanzu korona ta yi ajalin mutum 2,036 dagacikin mutum 162,275 da suka kamu da cutar a kasar nan.

Share.

game da Author