Rundunar ‘Yan sandan Jihar Sokoto ta tabbatar da kashe wasu mutum 10 da ‘yan bindiga suka yi a kauyen Tara dake karamar hukumar Sabon Birni.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ASP Sunusi Abubakar, ya ce baya ga mutum 14 da maharan suka kashe, wasu mutum 3 sun samu rauni, ana duba su a asibitin kashi dake Wamakko.
A ganawa da kwamishinan ‘yan sandan jihar yayi da mutanen garin Tara, ya bayyana cewa wannan hari ya bakanta mishi rai matuka.
” Ina kira ga mutane su ci gabada baiwa ‘yan sanda hadin kai domin kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
” Sannan kuma ina kira a gareku ku sa ido sosai kuna lura da shige da ficen mutane musamman wadanda ba ku san su ba domin kiyayewa daga fadawa tarkon muggan mutane.
A karshe ya ce an tura karin jami’an tsaro zuwa wannan kauye domin a bi sawun ‘yan bindigan da suka kashe mutum 10 a kauyen.