Yadda ‘Yar shekara 15 ta haifa wa jami’an kwastam biyu jariri daya a Katsina

0

Majalisar dokokin jihar Katsina za ta binciki wasu jami’an kwastam biyu da ake zargi da yin lalata da wata ‘yar shekara 15 har ta haihu.

Majalisar dokokin jihar Katsina za ta bincike wasu jami’an hukumar kwastam biyu da ake zargi da yi wa ‘yar shekara 15 fyade a jihar.

Shugaban kwamitin shigar da kararraki irin haka na majalisar Abduljalal Haruna-Runka ya sanar da haka ranar Alhamis a garin Katsina.

Haruna-Runka ya ce kungiya mai zaman kanta ‘Queen Dijah Women and Children Awareness Initiative’ ce ta kawo karan jami’an majalisar jihar.

A wasikar da Haruna-Runka ya karanta a zauren majalisAR wanda shugaban kungiyar Khadija Saulawa ta saka wa hannu ta roki kira ga majalisar ta yi bincike a kai.

Ana zargin jsami’an sun aikata wannan rashin hankali ne a rijiyar Hamza karamar hukumar Katsina.

Tun bayan zuwan wadannan jami’ai na Kwastan garin, suka rika ritsa wannan yarinya suna lalata da ita a cikin motan su kirar Toyota Hilux.

Yarinyar ta ce sukan bata naira 200 bayan sun gama lalata da ita. Haka suka rika yi har ciki ya shiga yarinya dai ta haihu da namiji.

Bayan haka wadannan jami’ai sun amince su rika baiwa yarinyar naira 15,000 duk wata domin dawainiyar kanta da na jaririn.

Sai dai kuma lamarin ya canja bayan an canja musu wurin aiki, sia suka daina biyan wadannan kudade.

Haruna-Runka ya ce kwamitin za ta gabatar da sakamakon bincikenta idan majalisar ta dawo hutu a Afrilu.

Ya kuma ce yayin da suke gudanar da bincike kwamitin za ta gayyaci jami’an kwastam din da yarinyar domin ji daga gare su.

Share.

game da Author