Wata matashiyar budurwa mai shekaru 18, ta kashe wanta da wuka daga tambayar ta inda ta fito a jihar Ondo.
Wani makwabcin wannan yarinya ya shaida wa manema labarai cewa, ita dai Idawo ta fice da ga gida ne kusa kwanaki hudu ba a san inda take ba.
” Toh bayan ta dawo gida ne sai wanta mai suna Kehinde ya tsare ta ya nemi ta gaya masa inda ta tafi kwana hudu bata gida. Daga nan sai Idowo ta fusata ta garzaya dakin dafa abinci wato kitchen ta dauko sharbebiyar wuka.
” Fitowanta ke da wuya sai ta daba wa kehinde wannan wuka a ciki.
Sai dai kuma rundunar ƴan sandan jihar ta shaida cewa ba a kawo karan kisan caji ofis ba.
” Hukumar tsaro ta Amotekun ne aka kai karar wannan aika-aika da aka yi. Saboda haka ba bu ruwan ƴan sanda a ciki yanzu.