Yadda tsadar kayan abincin ta buwayi duniya, watanni 9 a jere – FAO

0

Hukumar Samar da Abinci Bunkasa Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta bayyana nazarin da ta yi wa tsadar kayan abinci da kuma tashin farashin kayan abincin ya yawancin kasashen duniya.

FAO ta ce binkicken ta ya tabbatar da cewa tashin farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi ya tashi a cikin watan Fabrairum 2021.

Hakan ya na nufin kenan an tsafe watanni 9 farashin ya na hauhawa sama, bai sauko kasa ba.

Wannan bincike ya nuna kayan da su ka fi tashi sama sun hada da sugar da man girki.

Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta kara da cewa
farashin kayan abinci a watan Fabrairu ya tashi da kashi 2.4 fiye da watan Janairu. Wato kashi 26.5 bisa 100 fiye da farashin shekarar da ta gabata daidai wancan lokacin.

Yayin da farashin sugar ya tashi sama a cikin watan Janairu saboda yawancin kasashen da ke yin sugar sun kasa wadatar wa duniya sukarin.

Wannan karancin sukari kuma ta sa jama’a da dama shigo da sugar kasashen su daga Nahiyar Amurka.

“Daga cikin kayan da farashin su ya kara hauhawa a duniya, har da kwakwar man ja da mayuka da dama.

Haka nan kuma a kasashe da dama ciki har da Amurka, farashin seralak da cizi ya karu da kashi 1.2, kamar yadda a Afrika farashin jar dawa ya karu da kashi 17.4, saboda tsananin bukatar ta da ake yi a kasar Chana.

“Haka nan ma farashin masara da na alkama ya dan tashi amma kadan a yawancin kasashen duniya.” Inji rahoton.

Shi ma farashin naman miya da sauran naman kayan kwalama da tande-tande da lashe-lashe.

Yadda Farashin Naman Alade Ya Fadi A Duniya:

“Sai dai kuma abin mamaki shi ne yadda darajar namanalade ta fadi warwas a duniya, musamman a kasashen Turai.

Hakan ya faru saboda kasar Chana ta rage sayen naman da al’ummar kasar su ka yi.

Sannan kuma kasuwar naman alade ya fadi warwas a Jamus, ana barin masu sayar da nama da tulin naman alade babu mai saye.

Wannan lamari kuwa ya faru ne saboda wasu dalilai da su ka hada da haramta shiga da naman alade da aka yi a wasu kasashen Asiya da dama.”

Share.

game da Author