Sojojin Najeriya sun dakile yunkurin da wasu ’yan bindiga su ka yi domin su yi garkuwa dalibai a sakandare ta Turkish College, da ke unguwar Rigachikun, a cikin Kaduna.
Haka ya faru ne bayan da wasu ’yan bindigar su ka saci dalibai sama da 200 a Kwalejin Raya Gandun Daji, wato Federal College of Forestry Mechanization, da ke Afaka, cikin Karamar Hukumar Igabi, ranar Alhamis da dare, a Kaduna.
Daraktan Yada Labarai na Sojojin Najeriya, Mohammed Yerima, ya bayyana a ranar Juma’a cewa sojojin Najeriya sun yi gangami su ka kare Kwalejin Turkish daga afkawa hannun ’yan bindiga.
Sojojin sun samu wani kiran-kar-ta-kwana ne cewa su gaggauta kai agaji a Turkish College, wadda makaranta ce da babu ’ya’yan talakawa a cikin ta.
Jama’a da dama sun cika da mamakin jin yadda aka yi yunkurin satar dalibai a Turkish Collage, makarantar da ke cikin jama’a sosai.
Shugaban Majaliasar Dinkin Duniya, Gutteres ya yi Allah-wadai dakama dalibai a Kwalejin Kuma da Gandun Jeji a Kaduna.
PREMIUM TIMES ta ga sauran daliban da su ka rage a hannun masu garkuwa, ana gasa wa mata da mazan daliban ukubar dukan tsiya.
A cikin watanni uku dai an saci dalibai a makarantar Kankara a Jihar Katsina, Jangebe a jihar Zamfara, Kagara a jihar Neja da kuma Afaka a Jihar Kaduna.s