Yadda abokan Osinbajo suka yi wa mutanen Nasarawa ambaliyar ‘Goma Ta Arziki’ da tallafin kudade da ababen more rayuwa

0

A ranar 8 ga watan Maris ne kusan ƴan ƙananun ƴan kasuwa 50 suka samu tagomashi a garin Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa bayan da abokan mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo suka ƙaddamar da wani tsarin tallafi, na raba wa mutane N100,000 kowannen su domin taimakon masu ƙananan sana’o’i da talakawan garin.

Abokan Mataimakin shugaban ƙasa suna da’awar riƙo da manufofin farfesa Yemi Osinbajo ne tare da yaba masa kan salon shugabancin sa da ya ke samun buhubuhu na yabo da addu’o’i na musamman, da kuma yin tafiya da kowa ba yare da ya nuna banbancin addini ko na siyasa ba.

Babu shakka, dalilin da ya sa mutane ke daɗa ƙaunarsa bai wuce halayyarsa ta faran-faran da kuma kyautata zato ba. Matsayin a siyasance tun daga fari ya ba shi ƙima da sanya shi kasancewa ɗaya daga cikin ƴan siyasan da ake ƙona a ƙasar nan.

A ƙoƙarin taya shi murnar ranar haihuwarsa ta cika shekaru 64 a wannan shekara, abokan nasa sun antaya ne jihar Nasarawa, inda a nan ne mai girma Mataimakin Shugaban Ƙasar a watan Disamba, 2020 ya samu sarautar gargajiya ta ‘Madagun Jihar Nasarawa’ wanda a Turance ke nufin, ‘Leader and Captain.’

Babu abin mamaki a ciki kan dalilin da ya sa suka zaɓi Lafia domin yin murnar bukin idan aka yi la’akari da irin tarin ƙauna da goyon baya da kulawa da mataimakin shugaban ƙasar da kuma maigidansa, shugaba Muhammadu Buhari suke samu daga al’ummar garin ta Lafia.

Taron wanda aka gabatar da shi a fadar sarki ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da: Dr. Emmanuel Akabe, mataimakin gwamnan jihar da kuma manyan mutane daga ciki da wajen jihar waɗanda suka yi san-barka da yi wa mataimakin shugaban ƙasar addu’o’i na samun nasara kan abubuwan da ya sa a gaba.

An buɗe taron da addu’o’i ga mataimakin shugaban ƙasar tare da kuma iyalansa kafin fara ba da tallafin ga ƴan kasuwar tare da taya mataimakin murna kan zagayowar ranar haihuwarsa.

Sarkin Lafia, Mai Shari’a, Justice Sidi Bage Mohammad (rtd), ya yi masa addu’o’in na musamman da kuma fatan tsawon rai da zama cikin ƙoshin lafiya, nutsuwa da ɗaukaka ga mataimakin shugaban ƙasar wajen cigaba da amfanar da ƙasar da gogayyar da yake da ita.

“Ina mai maka fatan Allah ya ƙara maka tsawon rai da ƙoshin lafiya da wadata da biyan buƙata. Ina mai farincikin cewa barka da ranar haihuwarka,” in ji sarkin.

Sarkin dai ya bayyana mataimakin shugaban a matsayin mai tausayi da ƙanƙan da kai kuma ɗan ƙasa maras nuna ƙabilanci. Sannan ya yi addu’a kan ɗorewar zaman lafiya da haɗin-kai a tsakanin al’ummun ƙasar nan.

Babban mai masauƙin baƙi, mai girma Eng. A.A Sule wanda mataimakinsa, Dr. Emmanuel Akabe, ya wakilce shi, wanda ya yi maraba lale da abokan Osinbajo tare da yin godiya gare su bisa yanke shawarar zuwa Lafiya domin yin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar mataimakin.

Bayan tantance waɗanda za su ci gajiyar tallafin, abokan na mataimakin shugaban ƙasar, sun rarraba tallafin naira miliyan biyar ga mutane hamsin waɗanda yawancinsu mata ne da suka zo daga ƙananan hukumomi daban-daban.

Kowanne mutum ɗaya dai ya samu naira dubu ɗari. Wannan dai na ɗaya daga cikin yunƙuri na mataimakin shugaban ƙasar na ba da tallafi domin rage talauci a tsakanin alummar da kuma haɓaka tattalin arziƙi.

Har’ila yau, a ƙoƙarinsu na magance matsalar ruwan sha da shiyyoyi huɗu suke fama da ita, abokan mataimakin shugaban ƙasar sun gina fanfon burtsatse a Mararaba da Akunza da Kausakuwa da Ahuma da Kudancin Lafia.

Sannan kuma, sun raba keken ɗanki ga wasu da suka ci gajiyar shirin, inda sakataren ƙungiyar teloli, Safiyanu Abubakar, ya nuna farin cikinsu tare da gode musu kan wannan aikin lada. Ya kuma tabbatar musu da cewa za su yi amfani da su wajen haɓaka ƙananun kasuwanci.

A yayin magana a wurin taron, Osinbajo, wanda Malam Gambo Manzo, mai ba da shawara na musamman ga mataimakin shugaban ƙasar kan al’amuran siyasa, ya ja hankulan waɗanda suka ji gajiyar kan su mayar da hankali wajen yin abin da ya dace da kuɗin.

Kamar yadda ya faɗa, shirin an yi ne domin ƙarfafa wa masu ƙananun sana’o’i da talakawan futik wajen dogaro da kansu da kuma kaucewa tsammani na ayyuka masu romo.

“Mun gina rijiyoyin burtsatse a unguwanni huɗu a ƙarƙashin wannan masarauta da ba da jari na N100,000 ga mutane hamsin masu ƙananan sana’o’i domin bunƙasa kasuwanci da kuma dogaro da kai,” ya faɗa.

Hon Abubakar Sarki Dahiru, ɗan majalisa mai wakiltar Lafia Obin, wanda shi ne ya wakilci abokan Osinbajo, ya gode wa mutanen Lafia saboda fitowa da suka yi da kuma addu’o’i. Sannan ya bayyana cewa waɗannan fanfunan burtsatse an yi su ne kafin zuwa lokacin da za a jawo musu bututun ruwa zuwa unguwannin da abin ya shafa.

Hon. Hafeez Kawu wanda a yanzu ke wakiltar mutanen Tarauni a jihar Kano, shi ma ya yaba wa mataimakin shugaban ƙasar.

“Ya ɗauke ni tamkar ɗa ba tare da la’akari da bambanci na addini da ƙabila ba. Sannan ya kasance jan gwarzon shugaba. Muna fatan ubangiji ya ƙara lafiya,” ya faɗa.

“Mutanen da suka ci gajiyar waɗannan fanfuna sun cancanci hakan saboda ƙaracin tsaftataccen ruwan sha da ake fama da shi. Don haka, wannan shiri zai tabbatar da samuwar wadataccen ruwan sha. Saboda haka, wannan sadaƙatul jariya ce da kowa zai mora.”

Hadeeza Sabo Jibrin, shugabar Ƙungiyar mata ‘Yan kasuwa da Ƙungiyar Gamayyar Ƴan kasuwa na Musamman, a madadin waɗanda suka ci gajiyar shirin, ta gode wa abokan Osinbajo kan wannan tallafi, inda ta ce; “Mun yi farin ciki game da wannan tallafi kuma muna fatan hakan zai ɗore.”

Share.

game da Author