Kotun Koli ta sake tabbatar da hukuncin daurin shekaru 10 kan tsohon gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye, wanda babbar KotunTarayya ta daure kan wawurar naira bilyan 2.
An kama shi da laifin satar kudaden a lokacin da ya yi gwamnan jihar Filato tsakanin 1999 zuwa 2007.
Tsohon gwamnan wanda aka zabe shi sanatan Filato ta Tsakiya a zaben 2015, an daure shi shekaru 10 tun cikin watan Yuni, 2018, amma kuma ya kammala wa’adin sa na sanata a cikin kurkuku cikin 2019.
Dariye ya daukaka kara a Kotun Koli, sai da yayin da Manyan Alkali 10 su ka zauna kan sake duba hukuncin da aka yi masa na baya, sun soki hukuncin daya daga cikin tuhumar da aka yi masa mai dauke da hukuncin shekaru biyu a kurkuku.
Kenan Kotun Kolin a karkashin Mary Odili ba ta soke hukuncin daurin da ya fi yi wa na shekaru 10 ba.
Tun farko dai Babbar Kotun Birnin Tarayya Abuja, a karkashin Mai Shari’a Adebukola Bankojo ce ta daure Dariye shekaaru 14 a kurkuku a ranar 12 Ga Yuni, 2018.
Sai kuma wani daurin na shekaru biyu na daban.
Amma bayan ya daukaka kara, sai Kotun Daukaka Kara ta Abuja ta maida masa daurin daga shekaru 14 zuwa shekaru 10.