Wata wasika da ake yadawa a shafukan sada zumunta na yanar gizo a matsayin martanin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo dangane da halin da Najeriya ke ciki tsohuwa ce, shekaru biyu da suka wuce tsohon shugaban ya rubuta ta.
Tsohon shugaba Obasanjo ya rubuta wannan wasika mako guda bayan kisar Funke Olakunrin diyar jagoran yarubawan nan mai suna Reuben Fasoranti.
Kamar yadda yake a rubuce a wasikar, Obasanjo ya yi tir da rikicin Fulanin da ya addabi yankunan arewacin kasar, ya kuma zargi shugaba Buhari da ruruta wutar rikicin kabilanci. Wasikar ya kuma kara da baiwa shugaban shawara da “ya guji baiyana kansa a matsayin shugaban da ke hura wutar tsana, rashin kauna da tashin hankali.”
To sai dai binciken PREMIUM TIMES ya gano cewa rahotannin da ke fitowa dangane da wannan wasika ba gaskiya ba ne saboda ba a nan kusa-kusa ba ne nan Obasanjo ya rubata ta ba.
Tsohuwar wasikar da ya taba rubutawa ne a 2019 aka bijiro da ita kuma ake da yadawa.
Jaridar PREMIUM TIMES ta wallafa wasikar ranar 15 ga watan Yuli, 2019. A wasikar, Obasanjo wandatsohon shugaban kasar Najeriya ne tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 ya ce kasar nan ta shiga wani yanayi na tashin hankali da rikicin kabilanci tun bayan darewa kujerar mulki da Buhari yayi.
Mako daya bayan kisar Funke Olakunrin, diyar daya daga cikin shugabanin Yarbawa wato Reuben Fasoranti Obasanjo ya rubuta wasikar.
Wakilanmu sun ga wannan wasika kuma sun hada ta da wadda ta fito a 2019 sun ga cewa iri daya ce, dukkan su biyu.
Da muka tuntube shi ranar Talata makon Jiya, Kakakin shugaba Buhari, Kayode Akinyemi ya tabbatar mana da cewa wasikar dai itace wasikar da tsohon shugaban ya rubuta tun a 2019 wasu suka dawo da ita don wata manufa ta su dabam.