Ware dala bilyan 1.5 don gyaran matatar Fatakwal, ‘karambosuwa da kakuduba ce’ – Inji Atiku

0

“Wace irin toshewar-basira ce wannan a ce an ware makudan kudade wai za a kashe wajen gyaran matatun da ake kashe wa kudade a duk shekara, kuma sai asara su ke haifar wa tattallin arzikin kasar nan shekara da shekaru?”

Tsohon Mataimakain Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa sanarwar da gwamnatin tarayya ta yi wai za ta ware dala bilyan 1.5 domin a gyara matatar danyen man feteur ta Fatakawal, akwai zargi a cikin lamarin.

A ranar Laraba ce da Majalisar Zartaswa a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ta amince za ta sake narka har naira bilyan 600, kwatankwacin dala bilyan 1.5 wajen aikin gyaran matatar danyen mai ta Fatakwal.

Duk da Najeriya ta na da matatun mai har hudu, wadanda Shugaba Buhari ya yi alkawarin da ya hau mulki tun cikin 2015 zai gyara su, har yau shigo da tataccen fetur ake yi, duk kuwa da makudan kudaden da ake ci gaba da kashewa wajen gyaran su.

’Yan Najeriya sun yi ta yin taofin Allah-wadai da Allah-tsine dangane da sanarwar cewa za a sake narka naira bilyan 600 wajen gyaran matatar mai daya tal, wadda har yau ba ta daina cin kudade ba.

Ba a bar Atiku Abubakar a baya ba wajen caccakar wannan batu na kashe kudaden a gyara matatun mai, wanda ya ce ba abn amincewa ba ne, kuma akwai zargin harkalla a ciki.

“Ta ya za a ce za a kashe wadandan makudan kudaden wajen gudanar da aikin da babu tabbas, a daidai lokacin da kuncin rayuwa, karyewar tattalin arziki da tsadar abinci ke addabar jama’ar kasar nan.”

Ya ce a yanzu da ake ta hakilon neman ciwo bashin yadda za a tafiyar da ayyuakn gudanar da mulki da ayyukan raya kasa, ba daidai ba ne a ce gwamnati ta kwashi kudade ta fara gyaran matatar da ba ta da tabbas.

“Tun da farkoma tukunna, an shafe shekara da shekaru matatun man Najeriya na cin makudan kudade, sannan kuma ana ci gaba da narkar da wasu kudaden da sunan gyara. Amma a duk shekara dibga asara kawai ake yi a cikin su.

“Ba sau daya ba na sha bada shawarar cewa a damka wadannan matatun a hannun ’yan kasuwa, domin ta haka ne kawai za su iya aikin da ake so su yi, har itackan ta gwamnatin ta ci moriyar su.”

“Sannan kuma adadin kudaden da aka ce za a kashe wajen gyaran matatar, akwai wuru-wuru a ciki, saboda shekarar da ta gabata kamfanin Shell Petroleum ya sayar da Matatar Martinez ta California da ke Amurka a kan dala bilyan 1.2.

“Ya kamata kowane dan Najeriya ya kwana da sanin cewa Matatar Matinez ta Shell da ke California ta fi Matatar Fatakwal nesa ba kusa ba.

“Idan kutum ya kalli wadannan makudan kudaden, sai ya yi tambaya, shin an buga tandar neman kamfanonin da za su yi aikin gyaran, ko kuwa haka kawai aka zauna, aka kafci adadin makudan kudade aka ce za a narkas wajen gyaran matatar?”

Atiku ya kuma nuna matukar damuwa kan yadda za a kashe wadannan makudan kudade, a daidai lokacin da bashin da ake bin Najeriya ya tashi daga naira tiriliyan 12 zuwa naira tiriliyan 32.9 a karkashin mulkin Buhari.

Share.

game da Author