Wai da gaske ne akwai sabuwar cutar da ta bulla a China mai suna Nipah? Binciken DUBAWA

0

Wani mai amfani da suna (@isimaOdeh) a shafin Twitter, ya wallafa wani sako da ke zargin bullar wata sabuwar cuta a kasar China mai suna Nipah. Zargin ya kuma kara da cewa kasha 75 cikin 100 na duk wadanda suka kamu da cutar, na iya hallaka.

Tantancewa

Domin gano gaskiyar wannan batu, Dubawa ta fara da gudanar da binciken mahimman kalmomi a shafukan Twitter da Google. Binciken da ta gudanar a Twitter ya kaita wadansu shafukan da su ma suka sanar da bullar wannan cuta a China. Kamar yadda wadannan misalan suka nuna.

Binciken shafin google ma ya gano wadansu rahotannin, a ciki har da guda daga shafin BBC wanda ya baiyana cewa lallai bullar cutar ya janyo fargaba a nahiyar Asiya.

Mece ce kwayar cutar Nipah

Bisa ga bayanan Hukumar Lafiya ta Duniya, kwayar cutar Nipah (Niv) na daya daga cikin irin cututtukan da ake kamuwa da su daga jikin dabbobi. Masana kimiyya sun fara gano cutar ne a shekarar 1999 lokacin da ta barke a gonakin masu kiwon aladu a kasar Malaysia, sai kuma Bangladesh wadda cutar ta bulla mata a shekarar 2001 Bayan Bullar cutar ta kan sake dawowa a kowace shekara a kasashen. Haka kuma cuyar kan bulla a yankin gabashin Indiya tun bayan gano ko wacce irin cuta ce.

To sai dai duk da cewa kwayar cutar Nipah bata shafi kasashe da yawa a nahiyar Asiya ba, akwai barazanar cewa kasashe da yankuna wadanda basu taba samun cutar ba yanzu za su iya kamuwa da ita, tunda an tabbar akwai kwayar cutar a wasu dabbobin da ke rayuwa a yankunan musamman Jemage. Akwai kuma ire-irensu a kasashe da dama ciki har da kasashe kamar Cambodia, Ghana, Indonesia, Madagascar, Philippines da Thailand.

Kwayar cutar Nipah kan dauki tsawon kwanaki hudu zuwa 14 a jikin mutum kafin alamunta su fara bayyana a jikin dan Adam. Amma kuma akwai wasu rahotanni da suka nuna cewa cutar kan dauki tsawon kwanaki 45 a jikin mutum.

Yaya ake Kamuwa da cutar?

Ana kamuwa da kwayoyin cutar Nipah ta hanyar muamula da dabbobi ne. Ta wannan hanya ce ytake shiga cikin jikin dan Adam. Idan kwayar cutar ta shiga jikin mutum, a wasu lokuttan ba zai rika jin ciwo ko canji ba a jikin sa zai rika jin sa lafiya lau yake, amma kuma wani idan kwayoyin cutar suka shiga jikin sa sai ya rika jin ciwo a jiki, sannan kuma ya fara ji yankewar numfashi sannan kuma ana samun kumburi a kwakwalwa. To amma mahimman alamun da ke nuna bayyanar cutar sun hada da ganin jiri, gajiya da tabuwar hankali ko kuma fita hayyaci, da kuma alamun da ke nuna cewa akwai matsala a kwakwalwa.

Kwayar cutar na yi wa dabbobi lahani sosai musamman aladu abun da zai iya janyo wa masu kiwon aladu asara.

Alamun cutar?

Wadanda suka kamu da cutar su kan ji alamu kamar zazzabi, ciwon kai, ciwon jiki, amai da ciwon makwogwaro da kumburin kwakwalwa, da kuma mutum ya fita daga hayyaci.

Wadansu kuma sukan kamu da ciwon huhu da samun matsala wajen yin numfashi. Idan kuma ya taba ƙwaƙwalwa, mutum na iya dogon suma na sa’o’i 24 zuwa 48 da kamuwa da cutar.

Yawancin wadanda cutar ta taba kwakwalwarsu, sukan warke amma kuma tabuwar hankalin ba ya tafiya gaba daya.

Kashi 20 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar, bayan sun warke, cutar na iya dawowa. Idan har cutar ta barke a kasa ko yanki, ana kiyasin kashi 40 zuwa 75 cikin dari na wadanda suka kamu da ita na iya rasa rayukansu musamman idan babu kayayyakin aikin da ake bukata don shawo kanta.

Yaya ake gano cutar?

Ganin cewa alamun cutar ba a bayyane suke ba, idan mutum ya kamu da farko ba a ganewa. Wannan na iya kawo kalubale domin cutar na iya yaduwa ba tare da an gane ba. Bayan haka, ana iya samun jinkiri wajen daukan jini da gwaji wanda zai iya sauya sakamakon gwajin daga karshe.

Ana iya amfani da tarihin lafiyar mai dauke da cutar ne a gano ta. Sannan a dauki ruwan da ke jikin mutum a gwada.

Yaya ake warkar da cutar ko kuma yin rigakafin kamuwa da ita

A yanzu haka dai babu magani ko allurar rigakafin cutar Nipah. Sai dai Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanya cutar a cikin jerin cututtukan da ke bukatar cikakken bincike. Duk wanda ya kamu da cutar kan sami kulawa ta musamman, dan a tabbatar matsalar numfashi da na kwakwalwa ba su kai ga yin sallama da duniya ba.

A cewar hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta CDC a yankunan da aka samu barkewar cutar akan sanya matakan kariya da suka haɗa da yawaita wanke hannaye da sabulu, rage zuwa wuraren da ake kiwon aladu da jemagu, takaita cin ‘ya’yan itacen da ake kyautata zaton jemage ya taba. Sannan a guji taba jinni ko wani ruwan da ke fita daga jikin mutumin da aka san yana dauke da cutar.

A Karshe

Duk da cewa akwai kwayar cutar Nipah kuma kashi 40 zuwa 75 na mutanen da suka kamu da ita ka iya mutuwa, ba sabuwar cuta ba ce da ta yi mafari daga China. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an fara ganin cutar ne a shekarar 1999 a kasar Malaysia.

Share.

game da Author