Majalisar Diinkin Duniya (UN) ta na rokon duk mai hali ko wadata ya zuba taimako a gidauniyar neman tara dala byan 1 domin a taimaki akalla mutum milyan 6.4 wadanda rikicin Boko Haram da na ’yan bindiga su ka kassara a yankin Arewa maso Gabacin Najeriya.
Daga cikin wadannan mutum milyan 6.4, Majalisar Dinkin Duniya ta kara da cewa mutum milyan biyu din su sun gudu daga gidajen su, wasu ma an ragargaza masu gidajen.
Mafi yawan kudaden dai inji UN, za a yi amfani da su ne wajen ayyukan ceton dimbin rayukan jama’a a Jihohn Arewa maso Gabas, da su ka hada da Barno, Yobe da Adamawa.
Kakakin Yada Labarai na Ofishin Hukumar Kula da Bayar da Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, Jens Laerke, ya bayyana cewa irin kuncin talauci da azabar da jama’ar yankin wadanda rikice-rikice ya kassara su, abin tausayawa ne.
Ya ce su na bukatar dauki da agajin gaggawa, domin ruyuwar su dungurugum ta na cikin hatsarin gaske. Sannan kuma su na matukar bukatar agajin gaggawa.
“Ina tabbatar maku da cewa sama a mutum milyan daya a yankin Arewa maso Gabacin Najeriya na fuskantar matsananciyar yunwar da idan ba a yi gaggawar tallafa masu nan da ‘yan watanni ba, to abin zai yi muni matukar gaske.
“Za su afka cikin mummunan halin da shekaru hudu hudu baya ba a shiga a yankin ba. Hakan kuwa ya kara faruwa ne saboda ci gaba da rikicin da ake kara haifar da gujewa daga kauyuka da garuruwa, rasa muhalli da dukiyoyi, rasa iyayen da za su dauki nauyin kananan yara da kuma bala’in anobar korona da ya kara haifar da kuncin rayuwa.”
UN ta ce tsakanin watan Mayu zuwa Agusta, lokaci ne da dan abincin da aka noma, aka girbe ke karewa, duk za a cinye shi, kuma bai wadaci dimyoyin jama’a da ke zaman hannu-baka-hannu-kwarya.
Shi kuma jami’in Shirin Samar da Abinci na Duniya (WFP), Tomson Phiri, ya bayyana cewa yawan kashe-kashe ya sa jama’a sun kaurace wa ayyukan noma a yankin Arewa maso Gabas, har ta kai cikin shekaru 10 kusan kashi 90 bisa 100 na jama’ar yankin da abin ya fi shafa, sun shafe tsawon shekaru 10 ba su je aikin noma a gonakin su ba.
Ya ce idan aka tara kudaden, zaka kashe dala milyan 354 wajen samar da abinci, kayan gina jiki, inganta lafiya da sauran bukatun rayuwar yau da kullum ta dole.