TURA TA KAI BANGO: Buhari ya saka dokar hana shawagen jirgin sama a sararin samaniyar jihar Zamfara

0

Bayan kammala taron Kwamitin tsaro da aka yi a fadar shugaban Kasa ranar Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka tsauraran dokoki a jihar Zamfara domin fatattakar ‘Yan bindiga da suka sheke ayarsu a jihar da yankin Arewa maso Yamma.

Mai baiwa shugaban Kasa Shawara kan harkokin Tsaron Kasa, Babagana Monguno ne ya bayyana matsayar gwamnati a zantawa da yayw da manema labarai bayan taron.

” Daga yanzu ba a yardarwa wani jirgi yayi shawage ko ya ratsa ta sararin samaniyar jihar Zamfara ba, sannan kuma gwamnati ta hana ayyukan hako ma’adinai da ake yi a jihar.

Buhari ya ce” Ba za mu zuba ido, ana yi mana yadda aka so ba domin bata mana suna ta hanyar ayyukan hare-haren yan bindiga a kasar nan ba. Tura fa ta kai bango yanzu. Duk wanda ake zargi da hannu ko kuma ingiza tada zaune tsaye zai kuka da kansa.

” Duk wanda yake ganin shi shafaffe da mai ne zai rika ruruta wutar tada hankalin jama’a da hada wata alaka da ‘yan bindiga, dubun shi ya cika shi da’ yan bindigan yanzu zai.

Jihar Zamfara ta yi kaurin suna wajen ayyukan ‘yan bindiga a musamman yankin Arewa Maso Yamma.

Jihohin Kaduna da Katsina suma na fama da ire-iren wadannan hare-hare na’ Yan bindiga.

Da safiyar Talata ne aka sako daliban makarantar Mata dake Jangebe, Jihar Zamfara, bayan sun shafe kwanaki tsare a hannun ‘yan ta’adda.

Share.

game da Author