Gwamna Bello Matawalle na Zamfara, ya bayyana cewa wasu tubabbun ’yan bindiga su 30 ne jihar ta yi amani da su, wajen shiga tsakanin har aka ceto daliban sakandaren Jangebe.
Matawalle ya jaddada cewa ko kwandala jihar ba ta biya a matsayin kudin diyya ba
Haka gwamnan ya bayyana a wata hira da ya yi da Gidan Radiyon BBC Hausa da safiyar Talata, bayan an sako daliban su 279.
Ya ce akwai wasu kimanin tubabbun ’yan bindiga su 30 wadanda su ka karbi zaman sulhu, kuma su ka ajiye makamai.
To da wadannan tubabbun ‘yan bindiga ne su ka tattauna amincewa a saki daliban wadanda ‘yan bindigar da ba su tuba ba su ka yi garkuwa da su, tun a daren Juma’a daga Sakandaren Jangebe ta cikin Karamar Hukumar Talata Mafara.
Matawalle ya ce dukkan daliban su 279 su na nan lafiya kalau, kuma ba da dadewa ba za a hada kowace da iyayen ta.
Matawalle ya kara yin kira ga gwamnatin tarayya ta kara jami’an tsaro masu sa-ido da sintiri a makarantun da ba su da isassun tsaro domin kauce wa sake kwasar yara a yi garkuwa da su.
Sannan kuma ya ce daliban da aka sace in su 279 ne, ba 317 kamar yadda aka rika yayatawa ba.
Tun da farko dai ya yi bayanin cewa dalilin da ya sa ya fi amincewa a rika yin sulhu, saboda babu wadatattun jami’an tsaro ne kawai.