TSANANIN KISHI: An yi jana’izan Amarya Fatima da Kishiyarta ta kashe a Minna kwanaki 54 bayan aure

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja sun kama wata mata da ta kashe kishiyarta mai suna Fatima Ibrahim saboda tsananin kishin mijin ta ya kara aure.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Muhammad Adamu ya sanar da haka a hira da yayi da BBC Hausa ranar Laraba a garin Minna.

An ce amarya Fatima ta kira yar uwanta a lokacin da uwargidan da yan uwanta suka tirketa a daki rike da tabare ta ce mata ta na cikin wani hali, kafin ta iso gidan su taru sun kwabkwabdeta tabaren har fadi kasa ba rai.

Bayan Fatima ta fadi warwas sai suka cinna wa gidan wuta saboda a ga kaman gobara ce ta kama da ita a gida ya babbake ta.

Ya ce mijin matan da kansa ya kawo karar ofishin yan sanda sannan ya bayyana abinda ya faru.

Bayan haka mahaifin Fatima, Ibrahim Yahaya mazaunin jihar Katsina ya ce an daura auren Fatima kwanaki 54 da Suka gabata a Sabuwar Unguwa jihar Katsina.

Yahaya ya ce a ranar da ‘yarsa za ta gamu da ajalinta Fatima ta kira ‘yar uwarta a wayar salula tana cewa wani mumummunar abu zai faru da ita ta yi gaggawar kawo Mata dauki.

Adamu ya ce rundunar ‘yan sandan jihar za su ci gaba da gudanar da bincike akai.

Kara aure da maza ke yi na matukar tada mummunar kishi a tsakanin mata inda cikin dan kankanin lokaci idan ba akai zuciya nesa ba sai gaga mace ta aikata abinda har ta mutu tana dana sanin aikata shi.

PREMIUM TIMES HAUSA ta taba buga labarin yadda wata mata mai suna Hauwa ta kashe ‘ya’yan ta biyu saboda mijinta zai kara aure.

Hauwa mazauniuar unguwar Sagagi ne a jihar Kano sannan bayan ta aikata haka ta tafi gidan iyayenta ta zauna.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce zata cigaba da bincike akai.

Share.

game da Author