Wasu kwararrun jami’an lafiya sun yi kira ga gwamnati da ta inganta yin gwajin cutar tarin fuka da samar da maganin cutar.
Kwararrun sun ce yin haka zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar a kasar nan.
Jami’an lafiyan sun yi wannan kira ne bayan tashi taron shirye-shiryen ranar tarin fuka ta duniya ta shekarar 2021 da aka yi da manema labarai a Abuja.
Kodinatan Shirin dakile yaduwar cutar tarin fuka ta Najeriya (NTBLCP), Chukwuma Anyaike ya ce kamata ya yi gwamnati ta bada karfi wajen bada maganin da gwajin cutar.
“Tunda tarin fuka cuta ce dake yaduwa cikin kankanin lokaci kamata yayi gwamnati ta inganta yin gwajin cutar domin gano wadanda suka kamu sannan da basu maganin domin hana yaduwar cutar.
Rahotan ya nuna cewa kasashen duniya 9 da tarin fuka ya yi wa tsanani sun samu karuwa a yawan mutanen da suka kamu da cutar a lokacin korona daga kashi 16% zuwa 41%.
Wadannan kasashe sun hada da Bangladesh, India, Indonesia, Myanmar, Pakistan, Philippines, South Africa, Tajikistan da Ukraine.
Binciken WHO ya nuna cewa Najeriya na daga cikin kasashen duniya 30 da suka fi fama da cutar sannan a Afrika ita ce ta faro.
Sakamakon binciken ya kara nuna cewa duk shekara mutum 245,000 na mutuwa a dalilin cutar.
Mutum 590,000 na kamuwa da cutar sannan mutum 140,000 dake dauke da cutar kanjamau na kamuwa da cutar duk shekara a Najeriya.