Tantance gaskiyar zargin kama kwamishinan ‘yan sanda da hannu dumu-dumu wajen yin garkuwar da mutane – Binciken DUBAWA

0

Zargi: Mai amfani da shafin Twitter da adireshin (@SDiaso) ya wallafa hoton da ke cewa an kama wani mataimakin kwamishanan ‘yan sanda bisa zarginsa da hannu wajen yin garkuwa da mutane.

Ranar 12 ga watan Maris 2021 wani mai amfani da shafin Twitter, Soludo Diaso (@SDiaso) ya wallafa wani hoton mutumin da ake zargi mataimakin kwamishanan ‘yan sanda ne. Hoton na dauke da taken: “An kama mataimakin Kwamishanan ‘yan sanda na @Police NG bisa zargin garkuwa da mutane a Najeriya.”

A ranar talata 16 ga watan Maris, mutane kusan dubu biyar sun sake wallafa hoton, wasu fiye da dubu shidda kuma sun latsa alamar amincewa da labarin.

Tantancewa

Domin tantance wannan hoto DUBAWA ta fara da gudanar da binciken hoton a shafin hotunan google. Sakamakon wannan bincike ya nuna cewa tun shekara ta 2019 wannan hoton ke sahfin yanar gizo. Daya daga cikin rahotannin da aka samu daga binciken ya baiyana mutumin a matsayin Kingsley Udoyen wanda ‘yan sanda a jihar Akwa Ibom suka kama shi a watan Janairun shekara ta 2019 bisa zarginsa da kasancewa sojan gona.

‘Yan sanda sun kama Mr Udoyen ne dan ya na yaudarar jama’a a sunan shi mataimakin kwamishanan ‘yan sanda ne a jihar Akwa Ibom bayan ba haka ba ne. Kwamishanan jihar a wancan lokacin Musa Kimo ya bayyana Udoyen a gaban ‘yan jarida a hedikwatar ‘yan sanda a babban birnin jihar wato Uyo.

Mr Kimo ya ce ranar biyu ga watan Janairun 2019 ne aka kama Mr Udoyen wanda ke zama a gida mai lamba uku (3) a titin Stadium, Abak yayin da yake amfani da mukamin bogi wajen yin barazana da sata daga jama’ar al’umma ba tare da sun dago shi ba.

“A binciken da aka gudanar a gidan shi, jami’an ‘yan sanda sun gano wata ‘yar bindiga kirar Birtaniya, sai dai babu harsashi. An kuma ga hotunan manyan jami’an ‘yan sanda da rigunan ‘yan sanda guda uku da wasu takardu na bogi,” a cewar kwamishanan ‘yan sandan.

A cewar wata sanarwar ‘yan jarida da kakakin ‘yan sanda Mr Frank Mba ya gabatar, Kingsley Udoyen “sojan gona ne wanda ke karyar cewa shi mataimakin kwamishanan ‘yan sanda ne. An riga an gurfanar da shi a gaban kotun Majistran da ke Abak, jihar Akwa Ibom, inda ake tuhumarsa da aikata miyagun laifuka,” a cewar kakakin ‘yan sandan.

A Karshe

Hoton Twitter da ke zargin an kama mataimakin kwamishanan ‘yan sanda bisa zarginsa da hannu wajen yin garkuwa da mutane ba gaskiya ba ne. Kamar yadda bincike ya nuna, mutumin cikin hoton sojan gona ne da ‘yan sanda suka kama amma ba dan sandan da ke da hannu a garkuwa da mutane ba.

Share.

game da Author