TALLAFIN DANGOTE: Shin da gaske ne akwai tallafin da Dangote ke rabawa ‘yan Najeriya don rage radadin talauci? – Binciken Dubawa

0

Kamfanin Dangote na daga cikin manyan kamfanonin da suka shahara wajen sarrafa kayayyakin masarufi da na gine-gine a yankin kudu da Saharan Afirka.

A cikin rukunin Kamfanonin Dangote akwai kamfanin sarrafa siminti, akwai kamfanin sikari, gishiri, da sauran su. Aliko Dangote wanda shine wanda shine attajirin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirka ne shugaban wadannan rukunin kamfanoni.

Kamfanin Dangote na da ofisoshi a kasashe 17 na nahiyar Afirka sannan yana da gidauniya. Gidauniyar Dangote na mayar da hankali ne wajen inganta rayuwar jama’a a Afirka baki daya ta hanyar samar da shirye-shiryen kiwon lafiya, da na llimi da kuma na dogaro-da-kai.

To sai dai kwanan nan wani sako daga shafin yanar gizo ya bayyana a manhajan WhatsApp, yana cewa Kamfanin Dangote, ta hannun gidauniyarsa na raba wa al’umma kyautan kudi a matsayin wani tallafi don dogaro-da-kai. Sakon ya kuma bayar da adireshin wani shafin intanet inda ya bukaci jama’a da su shiga su yi rijistan kansu don samun wannan tallafi. Masu amfani da WhatsApp sun yi ta aikawa wannan sako sau da yawa musamman a kananan kungiyoyin da ke manhajan.

Da zarar mutun ya latsa adireshin shafin, zai tarar da sako kamar haka:

“Gidauniyar Dangote ta dukufa ne wajen inganta rayuwar mutane a nahiyar Afirka a fannonin kiwon lafiya, illimi, da aiyukan dogaro-da-kai.

Shafin na dauke da wani babban hoton da ke da tambarin gidauniyar Dangoten. Sannan a gaban hoton akwai wasu a tsaye, wai ma’aikatan kamfanin ne.

Tambayoyin da ke shafin dai sun bukaci duk mai sha’awan samun kudin ya bayar da cikakken suna da lambar waya. Sannan daga kasan shafin, akwai manufofi da kuma sharuddan gidauniyar.

Bayan mutum ya latsa adireshin da aka bayar, sai ya ga hoton ministar da ke kula da Harkokin Jinkai wato Sa’adiya Umar Farouq tana mikawa wasu mutane kudi. Daga saman shafin kuma an rubuta “Tallafin Gwamnatin Tarayya”. Bugu da kari, shafin ya bukaci mutane su amsa wasu karin tambayoyin da suka hada da aikin da suke yi da dalilin da ya sa suke bukatar kudin tallafin na Dangote.

Da zarar an cike wadannan tambayoyi, wani sabon shafin zai bayyana, wanda shi kuma ya bukaci mutum ya tura sakon zuwa ga wasu lambobin da ke amfani da manhajan WhatsApp kafin a bayar da kudin tallafin.

Ba wannan ne karon farko da ake danganta sako irin wannan da Dangote ba. A watan Yulin Shekara ta 2020, an yada sako makamancin wannan a manhajan WhatsApp mai cewa Dangote na raba Naira 15, 000 kowani mako a matsayin tallafi ga kowani matashi a Najeriya domin rage radadin annobar COVID-19. To sai dai bayan binciken da DUBAWA ta gudanarta gano cewa labarin karya ne.

Tantance gaskiyar sakon

DUBAWA ta fara da tuntubar kamfanin Dangote kan sahihancin shafin yanar gizon da ke dauke da wannan sako, da ma gaskiyar wannan magana na bayar da tallafi. Malama Hauwa Mohammed Bello daga sashen sadarwar kamfanin ta tabbatar mana cewa sakon karya ne, kuma shafin na damfara ce kawai. A cewarta “wannan damfara ne babu wani abu kamar haka.”

Bayan haka, mun kuma gano cewa shafin irin shafukan nan ne masu saka tallace-tallace, amma kuma suna boye manhaja mai lahani ga na’ura, irin wanda daga mutum ya latsa zai yi wa komfutarsa illa.Haka dai za ka yi ta fama da shiga nan, fada can, baka ga shafin caca ko tallar da baka san hawa ba baka san sauka ba.

Wani abun da ya sake tabbatar da rashin sahihancin shafin shi ne yadda ya kasa bambamta tsakanin labarin tallafin da Dangote ke bayarwa da na gwamnatin Tarayya. Duk da cewa labarin ya ce Dangote ne ke raba tallafin kudi, shafukan sun rika bayani ne a kan “tallafin gwamnatin tarayya.”

Bugu da kari, wani shafin bincike mai suna ScamDoc (wato wata manhajar da ke tantance sahihancin lambobi da adiresoshin yanar gizo ta kuma ba da amsoshi ga tambayoyin da masu amfani da yanar gizo suka fi yi kamar: Yaya ake sanin ko shafin yanar gizo sahihi ne?
Yaya ake tantance ko sakon email na yaudara ne?) ta bayyana cewa shafin bai fi wata shidda (6) ba da kirkirar sa, kuma yana hade da wani adireshin da ke danganta shi da shafukan da aka san su da yaudara a wasu kasashe, wadanda DUBAWA ta taba bincika a baya.

Daga Karshe

Ana yawan kirkirar shafuka irin wannan domin yaudarar jama’a. Mafarin wannan shafi shi ne ya sanya manhajar da za ta iya yi wa na’urar Komfutar ka illa. Bayan haka su kan su wakilan offishin Gidauniyar Dangote sun tabbatar mana cewa gidauniyar ba ta da wani shiri ko tsari na ba da tallafi a halin yanzu. Wannan magana na tallafi dai karya ce.

Share.

game da Author