TAKARAR 2023: Kwamiti na so PDP ta yi amfani da cancanta, ba karba-karba ba

0

Kwamitin Nazarin Zaben 20219 na Jam’iyyar PDP, ya shawarci jam’iyyar ta dubi cancanta wajen wanda za ta tsayar takarar shugabancin kasar nan a zaben 2023, maimakon a ce jam’iyyar ta bi tsarin karba-karba.

Kwamitin ya ce kamata ya yi a kyale duk wani mai bukatar tsayawa takarar shugaban kasa, ko ma daga wace shiyyar kasar nan ya ke, to ya fito takara kawai, sai cancantar mutum ta kai shi ga nasarar tsayar da shi.

Kwamitin wanda ya damka wa uwar jam’iyya rahoton sa a ranar Laraba, ya bayyana cewa, duk da mutane da daman a ganin cewa kamata ya yi a damka wa yankin Arewa maso Gabas ko Kudu maso Gabas takarar zaben shugaban kasa a zaben 2023 a karkashin PDP, to kamata ya yi a zabi cancanta kawai ba bangaren da mutum ya fito ba.

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ne Shugaban Kwamitin Nazarin Zaben 2019, kuma kwamitin sa ne ya bijiro da wannan shawara ga uwar jam’iyyar PDP ta kasa.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Enyinnaya Abaribe, tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, da Sanata Stelle Omu sai Emmanuel Agbo a matsayin sakataren kwamiti.

Idan har PDP ta yi amfani da wannan tsari na cancanta maimakon karba-karba, to za ta kashe kaifin wasu ’yan adawa masu hankoron a yi tsarin karba-karba, kuma a mika takarar shugaban kasa ga dan Kudu.

“Yayin da mu ka amince da masu cewa yankin Arewa maso Gabas da Yankin Kudu maso Gabas ba su dade kan shugabancin kasar nan ba, don haka a yi masu adalci a ba su takarar 2023, to kuma kada mu manta cewa kasar nan cike ta ke da wadanda su ka cancanta daga kowace shiyya.” Inji Bala Mohammded

“Sannan babban abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne a zabi shugaba wanda zai fitar da kasar nan baki dayan ta daga halin kaka-ni-ka-yin da ta samu kan ta ciki.

“Don haka mu ke ganin ya dace, kuma mu ke bayar da shawara cewa a bai wa duk kowane dan Najeriya ya zabi wanda ya fi cancanta ta hanyar gudanar da sahihin zaben fidda-gwani. Wannan hanya ce kadai za ta samar da kyakkyawan mataki rika samar da shugaban da ya cancanci jagorancin al’ummar Najeriya.”

Bisa ga yin la’akari da tunzirin da ya haifar da tarzomar #EndSARS watannin baya a Najeriya, wannan kwamiti ya shawarci uwar jam’iyyar PDP ta ware wasu mukamai ta ce na matasa ne da kuma mata kawai idan jam’iyyar ta yi nasara a zaben 2023.

Share.

game da Author