Akalla mutum 8,000 ne su ka kai kan su aka yi masu allurar rgakafin cutar korona, samfurin AstraZeneca a Najeriya.
Daraktan Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA), Faisal Shu’aib ne ya bayyana haka.
Da ya ke magana a wurin taron manema labarai na Kwamitin Shugaban Kasa kan Dakile Cutar Korona, a ranar Litinin, Shu’aib ya ce har zuwa yanzu dai babu wani rahoton wata matsala ko da daya tal a kasar nan, tun bayan da aka fara yi wa mutane rigakafin korona a kasar nan.
“Zuwa yanzu dai an yi wa fiye da mutum 8,000 allurar rigakafin korona. Kuma har yanzu babu wani wani rahoton wanda ya fuskanci wata matsala bayan an yi masa wannan allura. Amma za a iya fuskantar kumburar wurin da aka yi wa mutum allurar. Wannan kuwa ba wani abu ba ne.” Inji Shu’aib.
Ya kara da cewa h8ukumar sa ta NPHCDA na aiki kafada-da-kafada da Hukumar NAFDAC domin sa-ido kan allurar da kuwa wadanda ake wa allurar, domin ganin ko da za a samu wani rahoton wanda ya fuskanci wata matsala.
An fara gudanar da allurar rigakafin AstraZeneca a Najeriya ga jami’an lafiya masu fuskantar yiwuwar kamuwa da cutar, saboda cudanyar da su ke yi da marasa lafiyar da su ka kamu da cutar.
An kawo akalla kwalaben rigakafin AstraZeneca guda milyan 4 a Najeriya, wadanda tuni aka fara yi wa har mutum 8,000 ya zuwa yammacin ranar Litinin.
Gwamnatin Najeiya ta bayyana cewa ta na iyakar kokarin ganin cewa an dirka wa mutum milyan 106 allurar rigakafin a cikin shekaru biyu.
Sai dai kuma yayin da ake ci gaba da yin allurar ta AstraZeneca a Najeriya, wasu kasashe da su ka hada da Jamus, Italy, Faransa, Netherlands, Ireland, Austria, Afrika ta Kudu da sauran kasashe da dama irin sun dakatar da yi wa al’ummar kasashen su rigakafin AstraZeneca, biyo bayan rahotannin cewa allurar na haddasa toshewar magudanan jini a cikin jikin wanda aka yi wa allurar.
Discussion about this post