Sojojin Najeriya za su kwankwatse duk wata barazanar da matsalar tsaro ke wa kasar nan –Janar Attahiru

0

Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Janar Ibrahim Attahiru, ya bayyana cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da kasancewa gudumar kwankwatsar duk wata barazana da matsalar tsaro ke wa kasar nan.

Ya ce za su ci gaba da jajircewa wajen aikin dakile duk wata barazanar tsaro, kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya ba su umarnin ci gaba da yi.

Attahiru ya yi wannan jawabin kara karfin guiwa a lokacin da ya ke bayani wajen bude taron sanin-makamar-aiki na watanni ukun farkon shekarar 2021, wanda ofishin sa ya shirya wa jami’an sojoji, ranar Litinin a Abuja.

Ya ce Sojojin Najeriya su na da himma da jajircewa wajen ganin sun bi dukkan umarnin da Buhari ya ba su domin yi wa dukkan wata barazanar tsaro dukan-kabarin-kishiyar da za a magance matsalar baki daya.

Attahiru ya kara da cewa wannan taron sanin-makamar-aiki na watanni ukun farkon shekarar 2021, zai bayar da wata kafa da damar sake nazarin irin barazanar da yanayin wurare ke haifarwa wajen gudanar da ayyukan sojoji a sassa daban-daban.

Ya ce idan aka yi wannan nazari, za a kara gano wasu nakasu ko gibin da su ka kamata a gaggauta cikewa tare da shawo kan su ta hanyar tsare-tsaren da ake kan shirin yi a fafatawar da za a ci gaba nan gaba.

“Ina kara jaddada cewa Sojojin Najeriya a karkashin kulawa ta za su ci gaba da kasancewa masu kwankwatsar duk wata barazanar matsalar tsaro a kasar nan.

“A kan haka ina umartar dukkan cewa a rika maida hankali sosai wajen ganin ana ci gaba da samun irin gagarimar nasarar da mu ke kan samu a yanzu, har ma mu kara kaimin ganin samun fiye da wadda mu ke samu din a yanzu.

“Dukkan kwamandojin da ke bakin daga tilas su rika tilawar umarnin da na bayar wajen tabbatar da tilawar a aikace domin kara samun nasara tare himmar gaggauta kawar da duk wata barazana.”

Share.

game da Author