Sojoji sun ceto mutane 10 da ‘yan bindiga suka sace a kwatas din hukumar jiragen sama a Kaduna

0

Kwamishina Tsaro da Harkomin Cikin Gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa sojoji son ceto mazauna kwatas din ma’aikatan hukumar jiragen Sama dake Ifirah, Karamar hukumar Igabi jihar Kaduna.

Aruwan ya bayyana sunayen wadanda aka ceto kamar haka:

Mr. Ilori Sunday
Mrs. Celestina Sunday
Miss Beauty Oshaibie Sunday
Miss Miracle Sunday
Miss Marvelous Sunday
Miss Destiny Sunday
Mr. Samuel Sunday
Miss Deborah Sunday
Hajiya Badiyatu Abdullahi Gambo
Bilkisu Gambo

Gwamna El-Rufai ya jinjina wa sojojin bisa sannan gana da wadanda aka ceto, yana mai yi musu fatan alkahiri da yi musu jajen abin da ya faru da su.

Idan ba a manta ba ranar 6 ga Maris ne mahara suka afka cikin kwatas din suka sace wadannan mutane.

Tun bayan afkuwan wannan al’amari, sojoji da sauran jami’an tsaro suka fantsama domin ceto wadannan mutane da yin farautan yan bindigan.

Share.

game da Author